Umar A Hunkuyi" />

Gwamnan Taraba Ya Gargadi Sarakunan Gargajiya Da Su Nisanci Siyasa

Gwamnan Jihar Taraba, Darius Ishaku, ya gargadi Sarakunan Jihar da kuma sabbin dagatai 48 da aka nada kwanan nan a Jihar, da su nisanci shiga cikin harkokin siyasa, su kuma gujewa yin amfani da su daga son ran ‘yan siyasa a babban zaben 2019 da yake ta karatowa. Gwamnan ya yi wannan gargadin ne a jiya, wajen nadin sabbin dagatai 38 da kuma hakimai 10 a Jalingo, ya yi masu nu ni da cewa, Masarautun gargajiya wurare ne na samar da hadin kai, ba na raba kawukan al’umma ba.
Ya ce, “Ina son na gargade ku, da ku nisanci harkokin siyasa, musamman a wannan zaben da ke dada karatowa. A matsayinku na Sarakunan gargajiya, ya kamata ku rike matsayin naku na iyayen kasa, ku kuma rungumi kowa a wajen tafiyar da mulkin naku. “Matsalar rashin tsaro ce ta tilasta mana kirkiro wadannan masarautun da kuma daukaka darajar wadanda ake da su a baya, don haka ya zama tilas ku samar da zaman lafiya a yankunan naku.” Gwamnan ya bayyana cewa, kirkiro sabbin Masarautun yana daga cikin shirin gwamnatinsa na baiwa kowace kabila ‘yancin ta a Jihar.
Ya kuma yi nu ni da cewa, hakan kuma zai kara karfafa matsayin masarautun ne a Jihar, ya kuma magance kukan da wasu kabilun Jihar ke yi na an danne su. Tun da farko, Babban sakataren ma’aikatar kananan hukumomin Jihar, Bello Yero, ya bayyana cewa, sama da al’ummu 40 ne na Jihar suka ci wannan gajiyar na gwamnatin Jihar. Da yake na shi jawabin, a madadin sabbin dagatan, Hakimin garin Mutum Biyu, Ajhaji Mohammed Bose, ya gode wa Gwamna Ishaku ne kan nada su din da ya yi.

Exit mobile version