Gwamnan Zamfara Ya Aminta Da Mayar Da Kwamishinoni Uku Mukamansu

Gwamnan Zamfara

Daga Hussaini Yero, Gusau

 

Gwamnan Zamfara,Hon Bello Matawalle Maradun ya aminta da mayar da kwamishinoni uku mukamansu kuma za su ci gaba a ma’aikatansu.

 

Mukaddashin Sakataren Gwamnatin Jihar Zamfara, Kabiru Balarabe Sardaunan Dan Isa, shi ya bayyana haka a takardar da ya sanya wa hannu ya rabawa manema labarai a Gusau.

 

Wadanda aka mai da sun hada da Honarabul Ibrahim Muhammad Dosara, a matsayin Kwamishinan Yada labarai, sai Honarabul Sufyan Bashir Yuguda, a matsayin Kwamishinan Kudi, da kuma Honarabul Hajiya Fa’ika M. Ahmad, a matsayin Kwamishina Ayyukan Jin kai.

 

A cewarsa, Mai Girma, Gwamna Matawalle, ya kuma amince da mayar da Alhaji Abubakar Sarkin Fawa Dambo, a matsayin Shugaban zartarwa na Hukumar Jin dadin Alhazai. Sai kuma

Shekh Abubakar Muhammad Sodangi Gusau, a matsayin Shugaban zartarwa, Hukumar Zakka da Wakafi;

Ali Akilu Muhammad Dama, a matsayin Shugaban zartarwa, na Hukumar Kula da Haraji, a kuma mayar da su akan kujerarsa ya fara aiki nan take

Exit mobile version