Gwamnan jihar Zamfara, Hon. Bello Muhammad Matawallen Maradun, ya bukaci masu amfani da shafukan sada zumunta a jihar da su guji yada labaran karya saboda zai iya ruguza zaman lafiya kasar nan.
Gwamna Bello Muhammad yi wannan gargadi ne a lokacin da ya ke karbar bakuncin ‘ya’yan jam’iyyar APC karkashin jagorancin, Hon. Aminu Muhammad kaura, wadanda suka sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP a kwanan baya.
A jawabinsa Gwamna Matawalle ya bayyana cewa, akwai bukatar masu kula da shafukan sada zumunta a jihar dan su daina yada labaran karya a labaransu,saboda hakan na haifar da mummunar illa ga jihar da kasa baki daya. kuma mafi yawan mutanen da ke amfani da kafafen sada zumunta musamman matasa, suna bukatar yin amfani da shi yadda ya kamata ba rubuta san raiba da dan biyama wasu bukatunsu.
Matawalle ya ci gaba da cewa, yanzu haka kafofin sada zumunta na daya daga cikin manyan hanyoyin samun labarai amma babbar matsalarta ita ce yadda ‘yan kasa marasa kishin kasa ke amfani da shi ta hanyar karya, maimakon inganta hadin kai da ci gaban tattalin arziki.
Shugaban tawagar Hon Aminu kaura,ya bukaci Matasan da su taimaka wa gwamnati a dukkan matakai wajen ingantawa da fadakar da jama’a game da manufofi da shirye-shiryen gwamnati maimakon yada labaran da ka iya ruguza jihar
Kuma ya tabbatar wa Gwamnan Matawalle,cewa, Matasan masu hulda da kafafen sada zumunta ,zasu gyara kurakuran su da kuma daukar matakin akan masu neman kawo ma Jihar cikas ta hanyar kafafen sada zumunta.