Hussaini Baba" />

Gwamnan Zamfara Ya Jinjinawa Dr. Dauda Lawal Kan Tallafawa Ilimi

A Makarantar koyon Jinya da Unguwar Zoma, Dakta Dauda Lawal ya gina masu manyan gidajen kwanan dalibai guda biyu domin amfanin dalibai Maza da Mata .
Dakunan kwanan sun kunshi bangarori guda hudu a tsarin ginin sama da kasa. Kowane bangaren yana da dakunan kwana Takwas. Kowane daki kuma an sanya mai gadaje hurhudu masu daukar daliba biyu (wato dalibai Takwas kenan a kowane daki. Kuma an gina wurin wanka da bahaya a kowane daki. Haka kuma kowace Mace Takwas suna da dakin dafuwar abinci tare da Kantar ajiyar kayan abinci.
Sannan kuma dakunan wurin kwanan dalibai Mata dari Biyu da Hamsin da Shidda ne.a bangaren Maza dalibai Dari da Ashirin da Takwas ne za su amfana da wurin kwanan. Kafin samarda wannan alheri daga Dr. Dauda Lawal wanda aka kammala tun a shekarar bara dalibai Hamsin (50) Maza da Mata ne kawai ke samun wurin kwana a Makarantar.
A kwalejin kiwon lafiya da kimiya ta Tsafe kuwa, Dakta lawal Dare ya gina azuzuwa Tara kowanne dauke da duk kan kujerun su da tebura da duk abubuwan da ake sanya ma azuzuwan karatu ya sa yashi.
A Jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke Gusau kuwa, Titi ya yi masu mai tsawon kilomita biyu da rabi.
Wannan ne dalilin da ya sa Gwamna Matawale ya jinjinawa Dakta Dauda Lawal.
Sannan kuma gwamnan kuma ya yi kira ga masu hannu da shuni da su yi koyi da Dakta lawal Dare wajen samar da hanyoyin ci gaban jihar da ma kasa bakidaya.

Exit mobile version