Gwamnan Zamfara Ya Kaddamar Da Titin Kilomita 347.6 A Adamawa

Gwamnan jihar Zamfara Dakta Muhammad Bello Mutawalle, ya kaddamar da aikin hanya mai tsawon kilomita 347.6, a garin Kuba Gaya dake karamar hukumar Hong jiya Laraba a jihar Adamawa.

Hanyar wacce ta hade garuruwa da kauyuka sama da 300, bankin duniya da hadin gwiwar gwamnatin jihar Adamawa su ka gina, a sassan kananan hukumomin jihar 21.

Da yake jawabi a taron gwamna Mutawalle, ya godiwa gwamna Ahmadu Fintiri, da bashi damar kaddamar da aikin hanyar, ya ce duk da matsalar annobar korona da na ‘yan bindigar boko haram, bai hana gwamnan gudanar da ayyukan ba.

Ya ce “kamar yadda na san Ahmadu Fintiri, gwamnan talakawa ne, da idan kuka sake zabenshi a karo na biyu, zai ribanya ayyukan da yake yi yanzu haka” inji Mutawalle.

Da shi ma yake magana tunda farko gwamnan jihar Ahmadu Umaru Fintiri, ya ce aikin hanyoyin na daga cikin alkawarin da ya yi, lokacin yakin neman zabe, ya ce manufar gwamnatinsa shi ne kyautata rayuwar jama’ar karkara ta hanyar ingantattunMutawalle

Haka gwamna Fintiri, ya yabawa takwarar aikinsa na jihar Zamfara da halartan jihar domin kaddamar da hanyar, ya ce Adamawa da Zamfara na fuskantar matsalolin gudao iri guda, saboda haka ya ce suke aiki tare domin fuskantar matsalar.

Ya ce, “jihohin Adamawa da Zamfara, na fuskantar matsalar tsaro iri guda, don haka muke aiki tare, kuma za mu tabbatar mun magance wadannan matsalolin da mutanenmu ke ciki” inji Fintiri.

Haka shi ma da yake jawabi a taron, shugaban shirin bunkasa da gina ayyukan karkara (ADRMP-2) a jihar Adamawa Injiniya Zubairu Adamu, ya ce gina hanyoyin karkarar kan taimaka wajan fito da amfanin gona, da saukakewa mutane harkokinsu na yau da kullum, ya ce aiki ne da yake samun goyon bayan bankin duniya.

Ya ce “jihar Adamawa na cikin jihohin Nijeriya da yanzu haka RAMP-2 ta kammala dukkanin ayyuka da gyare-gyaren hanyoyi 347.6, wanda yau aka kaddamar da shi,” inji Zubairu.

Wasu daga cikin hanyoyin sun hada da Mildo da Kay,a Yinaku a karamar hukumar Madagali, da maahigar Kola-Boshikiri a Guyuk da Bakta a Shelleng, hanyar Numan/Biu a Numan, da Daba -Mayo Belwa, Polewire-Ndikong.

Wasun kuma sauran su ne Toungo-Kiri a Toungo, da Filingo, Parda -Muninga a Fufore, da Konan Yaji-Mijiwana Gilanbara a Gombi, Ribawo- Muchalla a Mubi ta arewa, Mayo Gule-Manjeken Salma a Maiha da Ngorore Mayo-Belwa, Gongoshi da sauransu.

Exit mobile version