Gwamnan jihar Zamfara, Dakta Bello Mohammed Matawalle, ya taimaka wajen ganin an ceto mutane 11 da a ka yi garkuwa da su ba tare da biyan kudin fansa ba.
Sakataren yada labarai na Gwamnan na Zamfara, Alhaji Jamilu Iliyasu Birnin-Magaji ya bayyana haka a takardar da yasanya mahannu ya rabawa manema lararu a Gusau babban birnin jihar Zamfara.
Da ya ke karbar wadanda lamarin ya rutsa da su, maza 10 da mace daya wadanda suka fito daga Karamar hukumar Bukkuyum ta jihar, gwamnan Matawale,ya bayar da tabbacin cewa, gwamnatinsa ba za ta huta ba har sai an samu cikakken zaman lafiya a dukkan sassan jihar.
Matawalle ya kara da cewa, kudirinsa shi ne tabbatar da dorewar zaman lafiya a duk sassan jihar da ma wasu sassan.dan samun dauwamammen zaman lafiya da tsaro a jihar.kuma yarjejeniyar zaman lafiya da sasantawa tare da ‘yan fashi da suka tuba za ta dmdore yayin da wadanda suka ki tuba kuma suka ki ajiye makamai za su gamu da fushin doka.
Tun da farko, yayin mika mutanen da aka sace su 11 ga gwamnan, kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, Alhaji Abubakar Muhammed Dauran ya ce,an kubutar da mutanen ta hanyar tattaunawar ba tare da biyan wadanda suka sace su kucin fansa ba.
Wadanda aka kubutar sun nuna matukar farin ciki da godiya ga gwamna Matawalle wanda suka bayyana a matsayin mai son samar da zaman lafiya da kuma kaunar dukkanin bangarorin mutane a jihar.
Idan ba a manta ba a ranar Alhamis din da ta gabata ne Gwamna Matawalle ya gudanar da wani taro kan tsaro tare da dukkanin masu ruwa da tsaki daga karamar hukumar Bukkuyum domin tattaunawa kan hanyoyin da za a bi wajen samar da zaman lafiya da lumana a jihar.