Gwamnati Ba Ta Girmama Kasuwanci – Hassan Adakawa

Daya daga cikin ‘yan kasuwar Sabon Gari da ke cikin birnin Kano, MUHAMMAD HASSAN ADAKAWA ya yi korafin cewa gwamnati ba ta girmama harkar kasuwanci, duk da kuwa yadda kasuwancin ke bayar da gudumawa wajen rage zaman banza ga matasa. A wannan tattaunawa da ya yi da LEADERSHIP A YAU a babban shagonsa da ke kan titin Naija a babban ginin da ke kallon tashar Malam Kato, dan kasuwan ya fara ne da bayyana mana tarihinsa a takaice. Ga yadda hirar

Daga Haruna Akarada, Kano

Da farko za mu so jin tarihin rayuwarka da gwagwarmayarka?

To da farko dai ni an haife ni a Unguwar Adakawa, wanda kuma a nan na rayu, na yi karatu har na karbi satifiket dina. Daga nan na fara harkar kasuwanci, yanzu na kwashe shekara ashirin ina zuwa kasuwar Saban Gari, wanda har Allah ya rayamu zuwa yau din nan, na san kasuwanci wani abu ne na hakuri.

Yaya ka kasance har Allah ya sa ka kai matsayin haka?

To, mun gode Allah, domin ka ga wannan lokacin abin da ake juyawa bai taka kara ya karya ba, amma yanzu cikin rufin asirin Allah, ka ga yadda abubuwa suka canja, an sami ci gaba na rayuwa sosai. Mu har kwanan gobe abin da muke fuskanta matsala ce guda daya, duk sanda mutum ya zo yana yin abu, dole gwamnati sai ta taimaki wannan tsari, in dai tana yi da gaske, in ta so a samu ci gaba. Ba wai wani abu ne ya sa na fadi wannan ba, a kasuwar Saban Gari za ka samu akwai mai Digiri akwai mai Difuloma, ko mai da ka sani akwai. In ba ka misali, idan za a ba da mukami sai a kawo wanda gwamnati take so, wanda kuma ba son harkar  kasuwancin yake yi ba, ba son komai ba, ya zo ai ta rigima da shi saboda  bai san yadda zai shawo kan matsalar ba.

Magana ta biyu, babu wata gwamnati da ke taimaka wa ‘yan kasuwa, tun da na taso haka ake, ba ci gaba har yanzu babu wani dan Majalisa ko na jiha ko na tarayya da zai ce ya kawo wani kudiri akan ‘yan kasuwa babu, shi kawai dai kasuwanci, Allah ne ke rike da shi, amma wallahi idan dai ta gwamnati ne, da yanzu mu ma almajirai ne.

Yadda ka dade kana karkashin wani, yaya zaman ya kasance?

Gaskiya ni dai shekara daya da rabi an gina min gida da mota aka ce ga ta nan na hau, tunda nake ban taba sayen ragon sallah ko ragon haihuwa ba, to in ya yayeni me zan je na yi? Ai wannan kyautatawa ce, idan ka ga ubangida da yaro ana samun matsala, to dama tun farko dama yana da matsala, amma mu sai godiya ga ubangiji, ni yanzu duk wani abu da ka sani yi min ake yi, hatta da kudin makarantar da na.

Yadda kuka shahara wajen harkar takalma, kuna yunkurin samar da injin yin takalma a nan kasar kuwa?

A’a, sai dai nan gaba, na san iyayen gidanmu suna fita ko’ina a duniya su kawo kaya a fadin duniya wannan maganar yin takalma, sai nan gaba duk irin kaya da suka kawo mu ne masu sai da shi.

Ganin cewa Nijeriya duk wani kaya sai dai a shigo da shi, ba a yi a gida, me yake jawo haka?

To ita Nijeriya sai dai mu kara wa Allah godiya, kuma mu ci gaba da addu’a, Allah ya kawo hazikan masu kishin kasa, wanda za su karbi kasar su yi mana abin da muke so. Bari in ba ka misali, Nijeriya idan ka ce kana so ka taimaka wa dan kasuwa, to ta wacce hanya?

Abin da ya sa na gaya maka haka, mu ne muke da ma’adanai a Nijeriya lokacin Janar Sani Abacha ya sa su Maigirma Dattijo Adahama suka je har Afirika ta Kudu suka lalubo ma’adanan da muke da su a nan kasar, amma abin da yake faruwa, in ba ka misali da jihata ta Kano, muna da ma’adanai, manya daga cikinsu, muna da guda talatin da hudu a Nijeriya, nan jihar Kano muna da kusan rabin wannan lissafin har yau babu wata gwamnati a nan jihar da ta yi tunanin ko da abu guda daya ne ta fito da shi.

In ba ka misali,

Muna da wani yashi a garin Danbatta, wannan yashin idan gwamnati ta je ta zuba hannun jarinta, nan da shekara goma ko ashirin wannan kadai zai rike jihar Kano. A cikin wannan yashin za ka yi gilas na ido, za ka yi gilas na saman agogonka, gilas na tebur, da za a bada himma akan wannan, to gwamnati ba ta bukatar neman wani tallafi ko rance a wani waje.

Amma gwamnatocinmu sun fi so su yi abin da za a kallesu a ce sun yi aiki ba, wanda talaka zai amfana ba, abin bakin ciki abin takaici wai jihar Legos ce ta zo da  wakilanta a siyar mata da daya daga cikin da ma da manmu na nan Kano asiyar ma ta tsawon shekara ashirin, ka ga komai aka samu ya zama ba namu ba ne. Daga nan Kano Gwamnanmu ya tashi wasu suka je Legos kan wannan Magana, inda Allah ya cecemu, akwai Shamsuddeen Usman, yana daya daga cikin wadanda suka je, bayan sun dawo suka gaya wa Gwamna gaskiya, suka ce in dai gaskiya ne, to wannan abin ya janye shi domin wannan abin ba mu ma da shi kwata-kwata.

To ka ga a ce ma’adananmu ba mu fito da su ba  sai ga wata jiha za ta kashe kudi wajen fito da ma’adanai, kuma duk kudi da wata jiha za ta kasha, Kano ma za ta iya kashewa. Ka ga mu a yanzu a jihar Kano, duk kasuwar da ka dauka a garin nan muna da kwararrun da za su iya komai a harkar gwamnati. Yanzu ‘yan kasuwarmu suna jin yare kala-kala, saboda tsabar fita waje, amma har yau gwamnati ma ta  yarda.

Ganin wannan magana da ka yi har ta tuna mana da gobarar kasuwa, ina aka kwana wajen biyan tallafi?

To akan wannan lamari sai dai mu ce Allah ya kawo sauki. Wallahi ni kaina ba zan ce maka ga iya adadin runfunanmu da suka kone ba a halin yanzu, amma saboda yawo da hankali, har yanzu ba wanda aka kula. Ba na mantawa, a Saudiyya an taba yin irin wannan wasu shekaru da dama, amma Hukumomi suka baiwa wannan bawan Allah da ya yi Riyal Milyan daya ya je ya yi gyare-gyare. Wannan kudin fa an ba shi ne kafin gwamnati ta zo ta tantance.

Amma mu ga shi ‘yan jihar Kano ne, wadannan ‘yan kasuwar kuma gobarar nan a jihar Kano aka yi, na san har yanzu akwai wadanda ba su gyara runfunansu ba, akwai wadanda sun bar kasuwar ma gaba daya.

Kana nufin har yanzu ba a ba ku komai ba?

Ai ko sisin-kwabo har yanzu. Ran nan mai girma Alhaji Bashir Usman Tofa ya kira ‘yan kasuwa ya ce gwamnati fa har yanzu ba ta bada komai ba, kuma ga tarin haraji, wanda idan ‘yan haraji suna zuwa wajenka, wani sai ka kasa gane na mene ne. Za su yi ta zuwa kala-kala, sanda muka yi gobara gwamnati da kanta ta ce ta yafe mana haraji na wannan lokacin, sai ga shi sun zo, ko ka biya ko a rufe maka shago.

Exit mobile version