Khalid Idris Doya" />

Gwamnati Na Asarar Naira Biliyan 300 Kan Cutar Maleriya

Hukumar da ke kula da fafutukar ganin an kawar da cutar Maleriya a Nijeriya, ta bayyana cewa; gwamnatin Nijeriya tana asarar Naira Biliyan 300 a duk shekara wajen yaki da cutar hade da yin aiki tukuru kan cutar ta maleriya.

Shugaban wannan hukumar na kasa, Audu Muhammad ne ya bayyana haka a wurin wani taron ‘yan Jarida na farko da aka shirya akan yadda za a yi amfani da sabbin dabaru wajen kawar da cutar ta Maleriya.

A lokacin da yake bayani akan rashin alfanun amfani da sinadarin Monethary wajen kawar da cutar ta Maleriya, Audu Muhammad ya bayyana cewa; Hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta shawarci a rika amfani da hadakar sinadaran Artemisinin.

Ya kara da cewa cutar Maleriya cuta ce wacce ake maganinta kuma za a iya kawo karshen illar da take haifarwa. amma duk da haka cutar nan ita ce babbar matsalar mutanen Afrika da Nijeriya baki daya kamar yadda yake bayyanawa. Ya kara da cewa irin wadannan matsalolin babbar barazana ne ga zamantakewa da kuma ci gaban tattalin arziki, inda kuma yake haifar da mutuwa da kashi 11, sannan ya ce kashi 30 na mutuwar Yara yana haifarwa.

Sannan ya jaddada muhimmancin kawo karshen wannan cuta ta Maleriya. hanyar da za a bi wajen cimma wannan manufar shi ne a hada hannu domin fuskantar matsalar tare kuma da samun kyakkyawan alaka na zamantakewa a tsakanin domin cimma gaci.

Audu ya daura da cewa, kashi 60 na masu zuwa asibiti zaka same su suna da cutar Maleriya. Ya ce; cutar tana haifar da rashin zuwan Yara makaranta saboda rashin wadataccen magunguna saboda kashi 13 zuwa 15 ne kawai ake iya magancewa.

Ya tabbatar da cewa; hukumarsa a shekarar 2017, ta raba ragar maganin cizon sauro guda miliyan 24 da dubu 519 da ]ari 371.

Ya ce yadda ake asarar kudi saboda cutar Maleriya, ya doshi Naira Biliyan 300 duk sheraka domin ganin an magance wannan cutar.

Ya ce kusan maganin wanann cutar Maleriya mai suna ACT Miliyan 130 aka raba a shekarar 2016, a inda a Oktoban shekarar 2017 aka raba guda Miliyan 25.4.

 

Exit mobile version