Gwamnati Ta Ɗauki Matakan Kare Mutuncin Noma —Barista Mai Yasin

Daga Balarabe Abdullahi,Zariya

 An shawarci gwamnatocin tarayya da kuma na jihohi da su ɗauki duk matakan da suka ga sun dace,domin kare mutuncin noma da ke neman ya durƙushe,a dalilin shigowa da wasu amfanin gona Nijeriya, musamman masara, da manoma suka noma ta fiye da ko wace shekara a daminar bana.

Wani fitaccen lauya da ke Zariya kuma babban manomi,mai suna Barista A Musa Aliyu.

Mai yasin ya bayar da shawarar a tsokacin da ya ke bayani akan matsalolin da suke neman durƙusar da sana’ar noma, musamman a jihohin arewa.

Ya ƙara jaddada cewar, duk wanda ke Nijeriya daga shekara ta 2015 zuwa yau, ya san matakai nagari da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ɗauka,ya zama sanadiyyar bunƙasar noma a sassa daban daban na Nijeriya, ba jihohin Arewa kawai ba.

Barista A Musa Aliyu Ya ce mataki na farko da ke neman durƙusar da noma shi ne, yadda gwamnati ta amince ko kuma ta sa ido, ana shigo da masara Nijeriya,wanda a cikin ƙanƙanin lokaci,darajar noman da aka yi,ya sami targaɗe, da ba a yi kuskure ba in an ce batun noma na gab da samun karaya.

Babban lauya Musa Aliyu, ya ce in har a na son a samu bunƙasar noma a Nijeriya, to da farko gwamnati ta dakatar da shigo da masara ƙasar nan, sai kuma ta ƙara mai da hankali wajen tallafa wa manoma da abubuwan da za su tallafa ma su wajen noman da suke yi, na damina ko kuma  rani.

Wannan tallafi da ya dace aba manoma, a ɗewarsa a bayar da tallafin a kan lokaci, musamman iraruwan shukawa ma su inganci da kuma maganin feshi, da shi ma babban al’amari ne, da tallafa wa manoman Nijeriya, su sami damar noma duk abubuwan da suke buƙata a gonakin su.

Babban manomi Barista mai yasin  ya ce, idan har aka tallafa wa manoma a kan lokaci, da kuma irin kayayyakin da za a shuka masu kyau, to manoman Nijeriya za su iya ciyar da Nijeriya da, abinci har ita ma ta riƙa fitar da abincin zuwa ƙasashen waje. Amma duk ƙasar da ba ta ciyar da kanta, sai ta dogara da wasu ƙasashen waje, wannan ƙasar ta na tsalle ne ta na dira a waje guda.

Daga ƙarshe  Barista A Musa Aliyu, ya shawarci gwamnonin Arewa 19 da su yi karatun ta-natsu kan halin da noma ke ciki, “su riƙa yin kasafi mai gwaɓi ga ɓangaren noma,kuma su tabbatar kasafin da suka yi,shi ake aiwatarwa’’ a cewarsa, in har gwamnonin Arewa suka canza salon tafiya,sana’ar noma za ta farfaɗo a ɗan ƙanƙanin lokaci da kowa zai yi mamaki.

Exit mobile version