Gwamnati Ta Ba Da Hutun Maulidi Ranar Talata

Daga Sulaiman Ibrahim,

Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Talata, 19 ga watan Oktoba a matsayin ranar hutu domin tunawa da ranar haihuwar Annabi Muhammadu (SAW).

Sanarwar da Babban Sakataren Ma’aikatar Cikin Gida, Shuaib Belgore ya fitar, ta bayyana cewa Ministan Cikin Gida, Rauf Aregbesola ne ya bayyana hakan a madadin Gwamnatin Tarayya,  ranar Juma’a a Abuja.

Aregbesola ya taya daukacin Musulmin Nijeriya na gida da na kasashen waje, murnar Eid-Mawlud.

Ya nemi ‘yan Nijeriya da su sanya ruhin kauna, hakuri da juriya wadanda su ne halayen Annabi mai tsira da amincin Allah, domin yin hakan zai tabbatar da zaman lafiya da tsaro a kasar.

Ministan ya umarci ‘yan Nijeriya, musamman Musulmai, da su guji tashin hankali, rashin bin doka da sauran ayyukan ta’addanci.

Exit mobile version