Daga El-Mansur Abubakar, Gombe
Mazauna Unguwar Arawa da ke yankin karamar hukumar Akko a jihar Gombe su na neman daukin gaggawa daga gwamnatocin jiha da tarayya, domin zaizayar kasa da ke unguwar na neman cinye mu su gidaje, wanda yanzu haka wannan kwarin da zaizayar kasar ta haifar ya tillastawa wasu sun fara barin gidajensu su na koma wa wasu unguwanni su na kama haya duk da irin tsadar rayuwar da a ciki.
Wani magidanci, wanda ya ke magana da yawun al’ummar Unguwar ta Arawa, Alhaji Salisu Dan-Iyan Arawa, shi ne ya bayyana hakan a lokacin da ya ke zantawa da Leadership A Yau ta Ranar Lahadi a Gombe, inda ya ce, wannan kwari ya na neman ya raba su da gidajensu tun fiye da shekara biyar wanda sun yi iya kokarinsu, amma har karfinsu.
Dan-Iyan Arawa ya ce, tun fiye da shekara biyar su ke ta kokarin ganin sun kashe wannan kwari ta hanyar cike shi da shara da tayoyin mota da sauran nau’o’in ciko, amma ya fi karfinsu, domin duk shekara kwarin karuwa ya ke yi ta kowacce gaba.
Alhaji Salisu ya kara da cewa, hanyar shiga unguwar tasu guda daya ce, amma ta hade unguwannin da yawa irin su Kagarawal da Malam Inna da Kundulum har Barikin Soja za ka je ta wajen, sannan ga shi kuma ta na neman katsewa ta raba wadannan unguwanni.
Ya ce, sun rubuta wa gwamnatin jihar Gombe takardar koke tun a karon farko, don ganin gwamna ya zo ya ganewa idonsa, domin a san yadda za a yi a magance wannan zaizayewar kasa, amma har yanzu babu labari, ya kuma ce sun kai kokensu ga ma’aikatar muhalli da kare Gandun Daji ma ta wajen kwamishinar ma’aikatar ko za su hada kai da gwamnatin tarayya a saka su a shirin nan na gyaran kwarurruka na New Map, amma nan ma abin ya ci tura.
Alhaji Salisu dan Iyan Arawa ya kuma ce, ruwan sama kamar da bakin kwarya da a ke yi irin na wannan shekarar ya sake kara kwarin, domin a ’yan kwanakin baya ma sai da wata mota ta fada kwarin da dare, wanda hakan ya daga mu su hankali sosai, domin da lokacin ruwa a ke yi, sai a rasa rai da dukiya.
“Bayan hanyar da ruwan ya saba bi yanzu haka ya sake canja wata hanya wanda ya sake raba unguwar gida biyu, inda kuma da ba don sharar da su ka dinga zubawa ba, da yanzu unguwar ba wanda zai iya saura a cikinta,” in ji shi.