Umar A Hunkuyi" />

Gwamnati Ta Bayar Da Kariya Ga Bincikar Kayan Atiku

Gwamnatin tarayya ta bayar da kariya a bisa binciken da jami’an hukumar tsaro na DSS suka yi wa Jirgin sama na musamman da ya dauko dan takaran shugabancin kasar nan a karkashin Jam’iyyar PDP a babban zaben 2019, Alhaji Atiku Abubakar, a lokacin da ya dawo cikin kasar nan daga binin Dubai, a ranar Lahadi.
Karamin Minista a ma’aikatar filayen Jiragen sama, Hadi Sirika, cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin manema labarai, James Odaudu, ya mika ta ga manema labarai tana cewa, “Hankalinmu ya kai ga martanin da ake yi a kan binciken da aka gudanar a cikin Jirgin Tsohon Mataimakin Shugaban kasan nan, Alhaji Atiku Abubakar, a tashar saukan Jiragen sama ta Nnamdi Azikwe, da ke Abuja, kwanan nan.”
“Muna son bayyana wa duniya cewa, binciken da aka yin da kuma maganan da Ministan ya yi ba su da wata alaka da siyasa, kamar yanda wasu ‘yan Nijeriya suke kuskuren fassarawa, aiki ne dai wanda aka saba gudanarwa kawai.
Ya ce, “In za a iya lura an gudanar da irin wanna binciken a Jiragen tsaffin mataimakan shugabannin kasar nan, wanda wannan aiki ne na doka kawai, ba wanda aka kebe a kan shi, sai dai Shugaban kasa, mataimakin shugaban kasa da shugabannin kasashen da sukan kawo ziyara kadai.”
“Kamar yanda dokar tsaro ta filayen Jiragen sama ta tanada, wadanda ba a bincikar su a duk lokacin fita ko shiga kasar nan kan wani aikin hukuma su ne, Shugaban kasa da tawagarsa, Mataimakin shugaban kasa da tawagarsa, shugabannin kasashe masu kawo ziyara kasar nan da tawagar su, kadai.”
Sirika, ya yi nuni da cewa, a bisa tsarin tsaron, ana bincikar Ministoci da sauran manyan jami’an gwamnati kamar yanda ake bincikar sauran fasinjoji.
Don haka a cewar sa, “Wannan aiki ne da aka saba da shi ga dukkanin manyan Jiragen saman da suke shigowa da fasinjoji cikin kasar nan, tilas ne jami’ai daga hukumomin, Kwastam, Shigi da fici, Lafiya, Tsaro, da masu lura da masu satan kudi su duba su.”
“A nan muna tabbatarwa da al’umma cewa, wannan ma’aikatar da sauran hukumomin da suke aiki tare da ita za su ci gaba da girmama shugabannin kasa, kamar yanda za su ci gaba da tabbatar da tsaron lafiyan tashoshin Jiragen namu.

Exit mobile version