Mustapha Abdullahi" />

Gwamnati Ta Bude Wa Masu Sana’ar Mota Wata Kafa – Nabarazil

Sana'ar Mota

Shugaban kungiyar masu sayar da motoci ta kasa reshen jihar Kaduna, Alhaji Ahmad Nabarazil ya yi kira ga Gwamnatin tarayyar Nijeriya da ta bude masu wata kafar da za ta ba masu sana’ar mota wata kafar shigo da motoci ta kasa.

“Hakika gwamnatin Nijeriya ta rufe wa masu sana’ar mota boda tun shekarar 2017, don haka muke kira murnar bude wannan boda da Gwamnati ta yi, kuma muna fata lamarin bude bodar zai shafe mu”, in ji shi.

Ya ci gaba da cewa, saboda tun da aka rufe Bodojin Nijeriya aka hana shigowa da dukiyoyin masu sayar da mota ta kan iyakoki, amma a yanzu tun da har an bude, muna fata a saka da mu a ciki.

“Kuma ba mun ki gwamnati ba ne, shi ya sa muke rokon gwamnatin ta san da mu, ta bude mana wata kafa da za mu rika biyan harajin shigowa da motocin, kasancewa kasa na bukatar kudi, kuma mutanen da suke a kan iyakokin nan da masu hulda da su duk suna bukatar a bude domin suna samun Taro da Kwabo ta hakan wajen shigowa da motocin nan. Don haka in an bayar da wata kafa ga masu sana’ar mota za a samu albarka kwarai.

Saboda haka muke yin kira ga gwamnati da kuma Hukumar Kwastan da su kawo wadansu tsare-tsaren da zai amfanar da kowa a kasa baki daya.

Muna kira ga shugabannin gidajen sayar da motoci da mabiyansu da su dukufa wajen yin addu’o’i, kasancewar kasar na bukatar addu’a ne kwarai.

Kamar yadda aka san masu sana’ar sayar da motoci masu biyayya ne tare da yin kawaici, abin da duk ba na alkairi ba, ba ka samun mai sana’ar mota a cikinsa. A saboda haka muna yin addu’ar Allah ya kara mana ci gaba da zaman lafiya a kasa baki daya.

Muna fata kada Allah ya maimaita mana irin wadansu matsalolin da suka faru a shekarar 2020 da ta gabata, kuma muna fatan dukkan alkairan da suka faru a shekarar baya Allah ya nunnunka mana su a wannan shekarar ya karo mana ci gaba.

Exit mobile version