Gwamnatin Tarayya ta umurci malamai a fadin Nijeriya da su ci gaba da amfani da Turanci a matsayin harshen koyarwa, inda hakan ke nuna bukatar fara amfani da harshen gida a wurin karantarwa bata karɓu ba.
Wannan matakin, an ɗauke shi ne don inganta koyo da kuma tabbatar da daidaito a koyarwar aji a duk fadin kasar.
- ‘Yansanda Sun Kama Mutane 4 Kan Zargin Fashi Da Makami A Bauchi
- Kashi 74% Na Marasa Lafiya Sun Gamsu Da Ayyukan Kiwon Lafiya Na Nijeriya — Minista
Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa, ya sanar da sauyin manufofin yayin da yake jawabi ga manema labarai a taron kasa da kasa na Harshen Ilimi na 2025, wanda Majalisar Burtaniya ta shirya a Abuja.
Taron ya hada bijiman masana, da masu tsara manufofi, da masu ilimi,da masu bincike, da abokan hadin gwiwa na haɓaka harkar ilimi daga Afirka, Kudancin Asiya, da Birtaniya don tattauna dabarun inganta ilimi ta hanyar harshe.
Dr. Alausa, ya jaddada cewa, yayin da kiyaye harsunan asali har yanzu yana da mahimmanci ga al’adu, amma Turanci ya kamata ya zama babban harshen koyarwa tun daga firamare har zuwa makarantun gaba da sakandare don inganta fahimta da gogayyar ilimi a tsakanin Daliban Nijeriya da takwarorinsu na duniya.













