Gwamnati Ta Kaddamar Da Zabgai Don Sama Wa Matasa Aikn Yi, In Ji Musajo (ll)

Ci gaba daga nako na jiya

Wasu na korafin cewar wannan jami’an tsaron gwamnati ba ta kawo su a farkon gwamnati ba, sai yanzu da muka doshi lokacin zabe wasu suna cewa kuna son amfani da matasan ne kawai don yin hidimar siyasa me za ka ce kan wannan?

Da zan so wadannan masu korafin ka same su idan akwai mai mata a cikinsu ka tambaye shi lokacin da aka shigo da matarsa cikin gidansa a lokacin take haihuwa? Me ye sa bai taba tambaya ba? mai ya sa ba ta haihuwa a ranar da ta zo ba? ai komai akwai lokacinsa, idan an ce mun dibi matasan ne don mu yi amfani da su a zabe ne, Yallabi gwamnatin PDP sun fi wannan gwamnatin kudi, sun fi su karfin mulki na sojoji, ‘yan sanda, cibil defence duk suna karkashinsu ina suka kai a lokacin zabe da aka kada su? Ai duk wanda ya ce maka mun dibi wadannan domin a taimaka a wajen zabe ne, wane taimakon za su yi? satar akwati? Satar akwatuna za su iya yi? kuma satar akwatin zai taimaka wa zabe? Wannan ba haka ba ne, ba mu kawo wannan ba, kuma kamar yadda na fada maka komai da lokacinsa, sai Allah ya nufa za a yi abu.

 

Kwanan nan gwamna ya ba ka wannan kujerar, akwai wani hubbasawa da kake da shi wajen inganta rayuwar matasa da mata ne baya ga wannan shirin da kuke yi a yanzu?

Sosai ma kuwa, na farko tukunna shi kansa wannan shirin muna son in da hali mu bunkasa shi ya fi haka, domin me ye sa yaranmu aka taimaka aka dibe su aikin nan, don haka muna son da yardar Allah za mu ga  yadda za mu yi mun bunkasa wannan tsarin mu kuma kara yawansu. Bar na baka misali, shekaran jiya (Na ranar da muka yi hiran da shi) na ke gani a tb jihar Kano wacce sun fi mu kudi, sun fi mu hanyoyin shigar kudi, sun fi mu karfin tattalin arziki, sun dauki ‘yan Bijiranti (Banga) su dubu uku da dari biyar 3,500 ne suka dauka amma kai tsaye suka watsa duk duniya suka gani a NTA, Sarkin Kano duk manyan nan suna wajen, to malam idan kano za su dauki 3,500 mu kuma Bauchi mun tsaya a 2000 ai mun yi kokari fiye da Kano kuma abun a yaba mana ne, kuma ma duk da hakan za mu kara adadin matasan nan.

Na biyu kuma akwai tsare-tsare da shirye-shirye da dan dama da za mu dauki matasanmu mu koya musu abun da za su zo su zama suna dogaro da kawukansu, za mu yi abun da turawa ke cewa za ku koya maka yadda za ka kama kifi amma ba za mu baka kifi ba; muna da irin wadannan tsare-tsaren da dama, yanzu akwai sanar dinkin takalmi, bar na baka misali ka ga ran-butttt (takalmin soja) din nan wadanda ‘yan Zabgai din nan suka yi amfani da shi suke kuma ma yin amfani da shi har yanzu irin wadanda sojoji ke sanyawa, wallahi a nan Bauchi aka dinka shi, a kasuwar Wunty, dukkanin yadda ka ga ya yi kyau a Bauchi aka yi.

Don haka za mu dibi yaranmu a koyar da su yadda ake hada takalma, ga nan idan ka je Jos, kaje Kofar Wambai a Kano duk irin takalman ake kawo mana nan wajen, don haka za mu yi kokarin koyar da yara wannan sana’ar na dinkin takalma kala-kala. Akwai tsare-tsare da suke kasa musamman na koyar da ababen da suka jibinsa sana’ar hanu da dama duk za mu yi wa matasanmu. Mata kuma su basu raina don haka ne muka fitar da tsari da za su bi mu baiwa mata jari a hanunsu kai tsaye, mai toyar kosai idan ka bata jarin dubu biyar ita ka bata jari sosai a wajenta, sannan akwai wasu wadanda tuni ma mun rigaya mun daursu kan koyon sana’o’i, wasu na koyan man shafawa, wasu na koyan gurguru, dinki, kai ga su nan abubuwan da suke koya da yawa. Abun da muke ta magana a nan shi ne ya kamata gwamnati ta shigo ta taimaka musu, ta yaya ne gwamnati za ta taimaka musu?

Misali, asibiti na gwamnatin jihar Bauchi ne, makarantu na sakandari na gwamnati ne ana yin zanin gado da su labulaye, ana sayan abun wanke bayan gida da sanyaya kamshin daki ko ofis don haka kada a je kano don sayo wadannan kayyakin, kada mu je Kaduna ko Legas, wadannan yaran da muka ba su horon a kira su a ba su aikin nan a kai kayyakin da ake so wajajen da ake so, in aka yi haka an bunkasa musu kasuwancinsu ko ya ya? Wannan shi ne tsarina, za yi zanin gado a asibiti to a bamu dama mu kawo telolin da suka kware wadanda za su yi zangin gadon nan kila ma fiye da wanda za a sayo a waje, ka da a je wani waje, idan ka bai wa dan nan yadin nan zai saye ne a nan ka ga harkar kasuwanci ya inganta.

 

Idan muka dawo dai kan wannan jami’an tsaron da kuka kafa, Bauchi an san ta da maganar ‘yan kwamitin unguwanni wasu lokutan a kan samu matsala a tsakanin jami’an tsaro a tsakaninsu da irin wadannan ‘yan kwamiti wanda hakan na biyo bayan zargin da jami’an tsaro ke yi wa ‘yan kwamiti na daukan doka a hanu wadanne matakai za ku dauka don kauce wa hakan a wannan hukumar ta ku?

Wannan tambayar ta ka, tana daga cikin hangen nesan da muka yi ya sa muka ce sai sun je an ba su horo a sanar da su ma su san hakkokin dan kasa a kan gwamnati, hakkin gwamnati a kan dan kasa, sannan kuma a koyar da su, su san iyakarsu, su san yadda za su yi su dauki doka irin wanda za su iya, akwai kuma kamen da in sun yi su kai ne ga jama’an tsaro fakak, har a ajin neman ilimi a ka sanya su domin koya musu kwas din Cibil Education dukka an yi hakan ne domin magance matsalar nan ta daukan doka a hanu wacce itace take yawon kawo rudani a tsakaninsu da jami’an tsaro; su ‘yan kwamiti na unguwanni har ga Allah suna taimaka wajen dakushe ‘yan kananan matsaloli na sace-sace da wasu matsalolin rashin kunya da suke faruwa a cikin al’umma, suna kokari sosai, amma wasu lokacin kamar yadda ka fada suna wuce gona da irin, suna samun hakan ne a sakamakon rashin horon da ba a yi musu ba, amma mu namu Zabgai sun samu horo kan yadda za su yi.

 

Exit mobile version