Gwamnati Ta Samar Wa Sarakunan Gargajiya Aikin Yi —Nwana

An bayyana cewar babakeren da turawa ‘yan mulkin mallaka ga tsarin sarautun gargajiya a kasar ya haifar da matsalar tsaro da ke zama barazana a halin yanzu. Wakilin Gwari-Nupe, Alhaji Muhammadu Awaisu Giwa Nwana ne ya bayyana hakan ga manema labarai a minna.

A cewarsa koda turawan mulkin mallaka suka shigo kasar nan sun iske mu da tsarin sarautun gargajiya amma hayen da suka yi ma tsarin yasa sarakunan mu suka zama ‘yan tallar muradun gwamnati maimaikon aikinsu na sanya ido a kasa. Yau masarauta tana amsar kashi biyar na kudaden da ke shigowa aljihun karamar hukuma, duk da hakan ba ta iya aikin komai wanda shi ya jefa sarakunan mu wajen kirkiro hanyoyin da za su samu kudade ko ta halin kaka.

Nwana yace tunda aka amshe shari’u da amsar haraji daga hannun masu unguwanni da dagattai zuwa hakimai ya kamata a kirkiro masu wasu ayyukan na al’umma, hakan ne zai iya ba su damar sanya ido akan kai komon baki a cikin jama’a, wanda rashin sanya idon yadda ya kamata shi ya jefa mu a cikin barazanar bata gari.

Gwamnatocin jahohi kan kashe makuddan miliyoyi akan tsaro amma sai ka ga yadda tsaro ke kara tabarbarewar ma kamar kawai hanya ce aka bude na wadata kai cikin sauki. A wata sai ka ji ana baiwa shugaban karamar hukuma miliyan biyu zuwa uku da sunan tsaro amma in ban da tsare kan shi ta hanyar samar wa kan shi kudaden shiga ba abinda suke yi.

Ya kamata majalisun kasar nan na dattijai da wakilai da su kirkiro doka wadda sarakunan gargajiya za su samu aikin yi. An nada mai unguwa bai da albashi kuma aikin jama’a ake son yayi, ta ina zai fara aikin, ko dagattai da ake biya albashi kudin bai wuce dubu talatin da biyu ba zuwa da biyar, shin in ban da su ‘yan maular siyasa me ake son su zama.

Yana da kyau in dai za a yi gyara da gaske, a tabbatar da sarakunan gargajiya sun bi ka’idar masarautu wajen nada rawunna, sannan ko wani basarake ya san aikinsa ba rabon gado ko rikicin fili kawai ba.

Ya kamata mai girma shugaban kasa, a matsayin shi na masani tsaro da ya tabbatar an bi duk hanyar da ta dace wajen a inganta tsaro a kasar nan, ana wasa da rayuwar jama’a wanda wannan kuskure ne ba babba kuma ba ana kokarin samar da zaman lafiya ba ne a irin wannan matakin. Ya kamata mai karamin karfi ya za mana yana da salama, mai kudin ma ya samu salama, ita kan ta gwamnati sai ta cigaba da ayyukan da ke gabanta.

Exit mobile version