Connect with us

LABARAI

Gwamnati Ta Ware Dala Biliyan 1.3 Don Muhimman Ayyuka –Lai Mohammed

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ware dala bilyan 1.3 (kimanin Naira bilyan 468), daga asusunta na waje domin aiwatar da wasu manyan ayyuka biyar.
Ministan yada labarai da al’adu, Lai Mohammed ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi a lokacin da ya bakunci wani shirin Talabijin na tashar Talbijin ta kasa mai suna, “Stepping Up”.
Ministan ya ce, ayyuka biyar daga cikin ayyukan da ake kan yin su, sun hada da, gina babban tagwayen hanyar Legas zuwa Ibadan, gina gada ta biyu a kan kogin Neja da gina hanyar da ta hada gabas da yamma.
Sauran biyun su ne, babbar hanyar Abuja zuwa Kano da aikin babbar tashar samar da hasken lantarki ta Mambila.
Ministan ya ce, gwamnatin ta Shugaba Buhari ta kuduri aniyar aiwatar da manyan ayyukan raya kasa a duk sassan kasar nan, za kuma ta ci gaba da kammala ayyukan da gwamnatin baya ta fara ta kuma yi watsi da su.
“Mun yi imani da cewa, a maimakon mu fari wasu sabbin ayyuka, zai fi amfanan ‘yan Nijeriya mu kammala masu dukkanin ayyukan da muka gada wadanda gwamnatin baya ta yi watsi da su.
“A shekarar 2014, gwamnatin nan ta kashe Naira bilyan 14 kan ayyukan sufuri, Naira bilyan 34 kan ayyukan albarkatun ruwa da noma da kuma Naira bilyan 106 kan ayyukan samar da hasken lantarki, ayyuka da gidaje.
A shekarar 2017, wannan gwamnatin ta kashe Naira bilyan 107 a kan ayyukan da suka shafi sufuru, Naira bilyan 130 a kan sha’anin noma da albarkatun ruwa, da kuma Naira bilyan 325 a kan hasken lantarki, ayyuka da gidaje.
“Gwamnatin a bisa wani abu da bai taba faruwa ba a tarihin kasar nan, ta batar da Naira tiriliyon 2.7 a kan aiwatar da manyan ayyuka a shekarun 2016 da 2017 kadai,” in ji shi.
Ya ce, gwamnatin ta kammala aikin hanyar nan ta Ilorin zuwa Jebba ta wuce Mokwa, wanda aka yi watsi da shi sama da shekaru 10.
Ministan ya ayyana ayyuka 69 daban-daban wadanda gwamnatin tarayya ke aiwatarwa a sassa daban-daban na shiyyar kudu maso gabashin kasar nan, ya kara da cewa, hakan yana kore karyan da ake shimfidawa na cewa wai gwamnatin ta yi watsi da yankin, wajen aiwatar da manyan ayyukan raya kasa.
Kan ayyukan sashen Jirgin kasa, Lai ya ce, a yanzun haka ana ci gaba da aikin gina titin na dogo mai tsawon kilomita 156 a tsakanin Legas zuwa Ibadan.
Ya ce, a watan Afrilu ne, gwamnatin ta sanya hannu kan yarjejeniyar karfafa titin Jirgin mai tsawon kilomita 3,500, da ta hada Legas da Kano.
Ministan ya ce, a kwanan nan ne shugaban kasa kaddamar da titin Jirgin mai tsawon kilomita 49.2 ta cikin garin Abuja.
Wanda wannan shi ne irin sa na farko a duk fadin nahiyar ta Afrika, a cewar shi.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: