Connect with us

LABARAI

Gwamnati Ta Yi Wa Gidajen Rediyo Da Talabijin Tayin Yafiyar Biliyan N7.8

Published

on

A matsayin wani shirin musamman na bayar da tallafin annobar Korona, gwamnatin tarayya ta yi tayin yin yafiya a kan kashi 60 na basukan da take bin gidajen Rediyo da Talabijin.

Gwamnatin tarayya tana bin gidajen yada labaran da abin ya shafa ne bashin da ya kai na Naira biliyan 7.8.

Dukkanin gidajen yada labaran da abin ya shafa an bas u sararin watanni uku domin su ci gajiyar yafiyar bashin.

Ministan yada labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed ne ya bayyana hakan a lokacin da ya ke ganawa da manema labarai a Abuja, tare da rakiyar babban daraktan hukumar yada labarai ta kasa, Farfesa Armstrong Idachaba.

Lai Mohammed y ace, kamar yanda hukumar kula da kafafen yada labarai ta kasa (NBC), ta bayyana, akwai gidajen rediyo da talabijin masu yawa na kasar nan da su ke fama da tsibigin bashi a kansu wanda gwamnatin tarayya ke bin su da har ya kai jimillan Naira biliyan 7.8.

“hakanan kuma da yawan kafafen yada labaran suna da masaniyar cewa ba za a sake sabunta lasisin na su ba kasantuwar dimbin basukan da a ke bin su.

“A kan hakan ne, hukumar kula da kafafen yada labaran ta NBC ta bai wa gwamnatin tarayya shawarar a yafe masu basukan, inda ita kuma gwamnatin tarayyan ta amince da hakan a matsayin wani mataki na kara karfafan kafafen yada labaran domin iya fuskantar matsalolin da su ka tsinci kansu a cikinsu a sakamakin barkewar annobar Korona.

“a) Yafiyar kasha 60 na dukkanin basukan da gwamnatin take bin kafafen yada labaran na kasar nan.

“b) Sharadin samun yafiyar basukan shi ne kafofin yada labaran da ake bi basukan su iya biyan sauran kasha 40 na basukan da ake bin su a cikin watanni uku.

“c) Duk wata kafar yada labaran da ta gaza iya biyan wannan sauran kasha 40 din da ake binta a cikin wannan damar ta watanni uku da aka ba ta, ta rasa wannan yafiyan na kasha 60 din.”

Dangane da bayar da tallafin ga gidajen wallafa Jaridu kuwa, Ministan ya ce, ya zuwa yanzun mu na kan tattaunawa ne da kungiyar masu wallafa jaridu da mujallu ta kasa domin sanin abin da ya kamata a yi masu a kan hakan.
Advertisement

labarai