Abubakar Abba" />

Gwamnati Tarayya Ta Fara Bunkasa Kiwon Zuma — Minista

Ministan Noma da raya karkara Cif Audu Ogbeh ya bayyana cewa, daya daga cikin matakan da Gwamnatin Trayya ta dauka don farfado da tattalin arzikinta itace ta bunkasa kiwon Zuma. Acewar sa, rashin samun tsayayyen farashin mai a kasuwar duniya wanda shine babbar hanyar samun kudin shiga ga gwamnatin tarayya ya janyo koma baya ga atattalin arzikin kasar nan, inda hakan ya sanya gwamnatin ta raba kafa wajen kiwon Zuma musamman don ta rage ta talauci a daukacin fadin kasar.Ogbeh ya sanar da hakan ne a taron baje koli na ApiEdpo Afrika na 2018 da aka gudanar a garin  in Abuja, inda kuma ya yi nuni da cewa, duk da daukin da gwamnatin tarayya ta samar har yanzu masu sana’ar suna gudanr da sana’ar a gargajiyance wanda ya kamata ne su fara sayar da ita. Ministan ya kara da cewa, “ naji dadi sosai dana tsaya a gabanku a wannan safiyar don yin bayani akan wanana  daya daga cikin matakin na raba kafa akan farfado da tattling arzikin kasar na kiwon Zumar.

 

Exit mobile version