Gwamnati Za Ta Fara Hakar Mai A Arewa Maso Gabas – Ministan Mai

Karamin ministan albarkatin mai na kasa, Timipre Sylva ya bayyana cewa, gwamnatin tarayya tana shirin fara hakar mai a yankin Arewa maso Gashin kasar nan.

Ministan ya bayyana hakan ne a wani hira da aka yi da shi a gidan talabijin da ke Abuja ranar Litinin.

“Na sha fadi cewa, mun gano mai a yankin Arewa maso Gabashin kasar nan, muna shirin fara aikace-aikacen hakowa tare da hadin gwiwar Lake Chad Basin.

“Ban san ta yankin da aka gano mai ba, amma a bangaren mun tabbatar da cewa a cikin karamin lokaci za a fara samar da mai a Arewacin kasar nan,” in ji shi.

Ministan ya bayyana cewa, cutar Koronaa ta yi matukar kawo koma-baya ga duniya a bangaren man fetur da kuma gas a fadin duniya.

Ya kara da cewa, a taron kungiyar kasashe masu arzikin mai wanda Nijeriya na daga cikin mamba wanda ya gudana ta faifan bidiyo a intanet, wanda aka tattauna matsalolin da cutar Korona ta haddasa a bangaren mai a kasuwan duniya a wannan lokaci.

Haka kuma, Sylba ya ci gaba da bayyana cewa, ‘yan fashin teku da masu fasa bututun mai wadanda suke da haramtattun matatan mai da ma wasu munanan ayyuka sun yi matukar raunata kasuwancin harkokin mai a shekarun baya.

“Kafin wannan lokaci, masu fasa bututun mai ake fama da su. Amma a halin yanzu an samu ragi na kasun kashi 50, ina tabbatar da cewa an samu raguwar fasa bututun mai a cikin kasar nan. Idan aka danganta shi da wanda ake yi a baya,  ina tunanin an saami sauki sosai.

“Na sani har yanzu akwai sauran masu fashin bakin teku, amma na san hukumomin tsaro suna aiki tukuru wajen dakile lamarin. A duk kullum mana daukan matakai da za su dakile duk wani rauni da muke fuskanta a wannan bangare,” in ji shi.

A bangaren gas kuwa, ministan mai ya bayyana cewa, gwamnatin tarayya ta dauki wasu matakai da za su kawo sauyi a bangaren gas a Nijeriya. Ya ce, an fara daukan wannan mataki ne tun lokacin da aka gyara bangaren mai wanda ya janyo karuwar farashin mai sakamakon yadda ake kayyade farashin bisa farashin danyan mai a kasuwan duniya.

Ministan ya kara da cewa, idan aka kwatanta da gwamnatocin baya ba wanda ba su kawo wani ci gaba ba a bangaren gas, inda a wannan  lokaci gas din Nijeriya ya yi karancin a yankin Afirka.

Ya ce, amma a halin yanzu an samu gagaruwar ci gaba a bangaren gas fiye da gwamnatocin da suka shude a Nijeriya. A cewarsa, an samar da gas wanda ya kai na kafa biliyan 222.34 a wannan watan, wanda ake iya samun kafa miliyan 7,411.52 a duk kullum.

A tsakanin watan Nuwambar shekarar 2019 zuwa watan Nuwambar shekarar 2020, an samu jimillan yawan gas da aka samar kafa biliyan 3,004.06, wanda ake iya samar da kafa 7,642 a lokacin wannan kididdiga.

A makon da ta gabata ce, kamfanin mai na kasa (NNPC) ya bayyana cewa, ya samu rabar naira biliyan 13.43 daga cikin kasuwancinsa na watan Nuwambar shekarar 2020, inda ya kai na kashi 54 idan aka kwatantashi da ribar da aka samu a watan Oktobar shekarar 2020 na naira biliyan 8.71.

Wannan yana daga cikin rahoton kudade da kamfanin NNPC wanda yake fitarwa a duk wata, kamar yadda jami’in yada rabarai na kamfanin, Dakta Kennie Obateru ya  bayyanawa ‘yan jarida a garin Abuja a makon da ta gabata.

Wannan yana nuna cewa, ana samun farfadowa a cikin bangaren mai da gas a Nijeriya, sakamakon matakan da gwamnatin tarayya take dauka a wannan fanni.

 

Exit mobile version