Connect with us

RIGAR 'YANCI

Gwamnati Za Ta Farfado Da Ayyuka Miliyan Biyar Bayan Korona

Published

on

Ministan Masana’antu, Kasuwanci da harkokin zuba jari, Adeniyi Adebayo, ya bayyana a karshen makon nan cewa gwamnatin tarayya za ta kirkiro tare da samar da ayyuka akalla milyan biyar a bisa wasu tsare-tsarenta na farfado da tattalin arziki.

A cewar Ministan, akwai wasu tsare-tsaren da gwamnatin ke yi na ceto ayyuka akalla milyan 1.4 a nan Nijeriya, inda akalla kashi 40 daga cikinsu duk mata ne masu kanana da matsakaitan sana’o’i da kuma akalla kashi 10 na wasu masu bukatu na musamman.

Ministan ya yi nuni da cewa wannan wani sashe ne na kokarin da ma’aikatarsa ke yi wajen jagorantar shirin gwamnatin tarayya na farfado da tattalin arziki a bayan kwaranyewar annobar Korona.

Duk wadannan tallafin za su kirkiro tare da samar da akalla ayyuka milyan biyar.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: