Gwamnati Za Ta Kashe Biliyan N71 Wajen Kwangilar Titinan Dogo Shida

Layin Dogo

Gwamnatin tarayya za ta kashe kudade wajen gudanar da hanyoyin jiragen kasa guda shida  a fadin kasar nan, wanda za su lakume naira biliyan 71.15 a cikin wannan shekara. Haka kuma, za ta kara kashe naira biliyan 15.1 wajen bayar da tsaro wajen kwangiloli da tashoshin jiragen sama da gine hanyoyi a filayen jiragen sama da sauran gine-gine a bangaren tashoshin jiragen sama a shekarar 2021. Rahoton kwangilolin da aka zaba a cikin kasafin kudin shekarar 2021 daga ma’aikatar kudi da kasafi da tsare-tsaren kasa ta tarayya da ke Abuja ta nuna a cikin sashin ayyukan bangaren jiragen kasa, wanda gwamnatin tarayya za ta kashe kudade wajen gudanar da kwangilolin titunan jiragen sama guda shida a wannan shekarar.

Gwamnati tarayya ta bayyana cewa, ayyukan jiragen kasan da za a kashewa naira biliyan 71.15 sun hada da aikin jirgin kasa daga Jihar Legas zuwa Jihar Kano da Kalabar z uwa Legas da Ajaokuta zuwa Itakpe zuwa Aladja  daga Warri. Sauran sun hada da na Fatakwal zuwa Maiduguri da Kano zuwa Katsina zuwa Jibiya zuwa Maradi na Jamhuriyar Nijar da Abuja zuwa Itakpe zuwa Aladja zuwa matatan main na Warri. A halin yanzu ana ci gaba da gudanar da ayyuka wadannan wurare, yayin da sauran sababbin har yau ba a fara su ba.

Ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya bayyana cewa, aikin jirgin kasan da ake yi a halin yanzu haka daga Legas zuwa Kano za a hade shi har zuwa Ibadan, wanda zai ci dala biliyan 5.3. A ranar 9 ga watan Junairun shekarar 2021, Amaechi ya bayyana cewa za a  kaddamar da gina titin jirgi a tsakanin Ibadan zuwa Kano dazarar gwamnatin tarayya ta samu bashin dala biliyan 5.3 daga gwamnatin kasar China.

“Muna ciran gwamnatin kasar China ta amince da bai wa Nijeriya bashin dala biliyan 5.3 domin gina titin jirgin kasa tun daga Ibadan har zuwa Kano. Tun shekarar da ta gabata gwamnatin tarayya ta aminci da bayar da kwangilar,” in ji minista.

A halin yanzu dai, wasu ‘yan tsirarun ayyukan titin jirgin kasan ana ci gaba da karubalantarsu wanda mafi yawancin ‘yan Nijeriya ayyukan na da ayar tambaya. Alal misali, aikin titin jirgin kasa tun daga Kano zuwa Katsina zuwa Jibiya zuwa Maradi da ke Nijar wanda gwamnatin tarayya ta bayar tun a ranar 11 ga watan Junairun shekarar 2021 a kan dala biliyan 1.96. Amaechi shi ya rattaba hannu a kan yarjejeniyar aikin, yayin da shugaban kamfanin Mota-Engil, Antonio Gboea ya rattaba hannu a madadin  kamfanin da zai yi aikin. Kwangilar titun jirgin kasan wanda ya hade Nijeriya da Nijar, wanda zai ci dala biliyan 1.96 da ke Arewakin Nijeriya wanda zai zagaye jihohi guda uku. Wadanda suka hada da Jihar Kano da Jigawa da kuma Katsina da ke da tsawon kilomita 283.75, wanda shi ne zai shiga har zuwa Maradi da ke cikin kasar Nijar.

Shakataren kungiyar Yarbawa, Yinka Odumakin ya bayyana waa manema labarai cewa, abin takaici dai shi ne, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fi mayar da hankali a aikin a wajen Nijeriya fiye da na cikin gida wanda ake fama da lalatun hanyoyi a Nijeriya.

Odumakin ya ce, “wannan abun takaici ne. Mun san irin halin da hanyoyin Nijeriya suke ciki. Idan muka duba babban hanyar Legas zuwa Ibadan da hanyoyin zuwa Yammacin kasar nan zamu ga dukkan su sun lalace sosai.

“Buhari ba ya yin abin da ya wajaba ga kasar, idan ba haka ba ai bai kamata a ce ya yi aiki har zuwa Maradi da ke Jamhuriyar Nijar. Ya fi bukatar Funili wadanda ba ma ‘yan Nijeriya ba fiye da ‘yan Nijeriyan.”

Exit mobile version