Yusuf Shuaibu" />

Gwamnati Za Ta Magance Matsalar Rashin Aikin Yi Tsakanin Matasa — Lai

Aikin Yi Tsakanin Matasa

Ministan yada rabarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed, ya bayyana cewa, gwamnatin tarayya za ta ci gaba da magance matsalolin rashin aikin yi a tsakanin matasa. Mohammed ya bayyana hakan ne ga manema labarai jim kadan bayan fitowa daga tattaunawa da gwamnoni da ministoci da shugabannin gargajiya na yankin Kudu Maso Yamma, bisa tashin hankalin da ya faru na zanga-zangar EndSARS wanda ya gudana a Jihar Legas.

Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa, an gudanar da taron kawana daya wadanda ya samu halartar wakilan shugaban kasa, wanda shugaban ma’aikatan fadar gwamnati Farfesa Ibrahim Gambari ya jagoranya.

Ya bayyana cewa, gwamnati za ta ci gaba da warware matsalolin matasa wadanda suka hada da zaman kashe wanda da kawar da talauci. Ya ce, gwamnati ta ware makudan kudade domin samar wa matasa ayyukan yi. Ya ce, a yanzu haka gwamnatin tarayya ta ballo da wani shiri da zai bunkasa harkokin kasuwanci. Mohammed ya ce, makasudin wannan taro na yankin Kudu Maso Yamma dai shi shi ne, bai wa gwamnoni da shugabannin siyasa da ke yankin damar tattaunawa. Ya kara da cewa, wakilan gwamnatin tarayya suna yi amfani da wannan dama wajen jajantawa gwamnatin Jihar Legas a kan tashin hankalin da ya faru sakamakon zanga-zangar EndSARS.

“Wannan taro ne na zaman lafiya wanda gwamnatin jihar da kuma gwamnatin tarayya suka amince da biyan bukatun masu zanga-zangar EndSARS,” in ji minister.

Ministan ya ci gaba da bayyana cewa, gwamnati za ta ci gaba da zuba jari domin bunkasa rayuwar mutane tare da aiwatar da tsare-tsaren bunkasa tattalin arziki wanda zai gina kasar nan da samar da kayayyakin more rayuwa ga ‘yan kasa da zai inganta rayuwar mutane.

Tun da farko dai a wurin wannan taro, shugabanin gargajiya na yankun Kudu Maso Yamma sun zargi ‘yan siyasa da yin amfani da zanga-zangar EndSARS wajen tayar da hankular mutane a yankin. Shuwagabannin gargajiyar sun nuna rashin jin dadinsu ta yadda ‘yan siyasa suke daukan nauyin masu zanga-zanga wajen ba su kudade domin su cimma burikansu na siyasa. Sun bayyana cewa, rashin ayyukan yi a tsakanin matasa ya yi matukar tasiri wajen ruruta wutar zanga-zangar EndSARS.

“Ya kamata gwamnoni su dauki matakan da suka dace a wajen wannan taro.  Gwamnonin sun nisanta kansu daga mu shugabannin gargajiya. Bai kamata a ce sai zabe ya karato ba sai a tuna da mu. Ya kamata a dunga gudanar da irin wannan taro akai-akai.

“Mun san abubuwa mai kyau da marasu kyau a cikin al’ummarmu,” in ji Ooni na Ife, Oba Enitan Ogunwusi.

A nasa jawabin, sarkin Oyo, Oba Lamidi Adeyemi, ya bayyana cewa, wannan tashin hankali ya kawo koma-baya ga yankin.

“Yaranmu ba su da ayyukan yi idan wasu da dama suke fama da talauci da yanwa. Matsaloli sun yi wa jihohin yawa.

“Jihojin ba su da ‘yancin kansu. Yanayin yadda muke gudanar da rayuwa a Nijeriya ba zai bar gwamnonin su tabuka wani abun kirki ba a jihohinsu,” in ji shi.

Shi kuma Oluigbo na Ugbo, Oba Akinruntan Obateru, ya bukaci shugaban rundunar ‘yan sanda  ya gudanar da cikakken bincike a kan lamarin tare da gurfanar da wadanda suke da hannun wajen ruruta wutar rikicin wanda ya biyo bayan zanga-zanga.

Sarkin Legas, Oba Rilwan Akiolu ya bayyana cewa, maganar gaskiya dai shi ne, mafi yawancin matsalolin ‘yan siyasa ne suka haddasa shi.

“Karfin ikon gwamnatin tarayya ya yi matukar yawa. Akwai bukatar a yi gaggauta garambawul ga jami’an tsaron kasar nan.

“Muna da matsalolin tsaro a Jihar Legas da kuma na yawaitar rashin ayyukan yi. Dole ne ba za a zauna lafiya ba mutukar matasa suna ci gaba da zaman kashe wando. Abin da ya faru dai ya samo asali ne daga rashin tsaro. Gaba daya tsarin yana bukatar a yi masa garan bawul,” in ji  Akiolu.

Exit mobile version