Yusuf Shuaibu" />

Gwamnati Za Ta Samar Wa Matasa Miliyan Biyar Ayyuka A Bangaren Lantarki

Bangaren Lantarki

Ministan wutar lantarki, Injiniya, Sale Mamman, ya bayyana cewa, gwamnatin tarayya ta na shirin samar wa matasa miliyan biyar ayyukan yi a bangaren wutar lantarki. Ya bayyana cewa, za a samu wadannan ayyuka miliyan biyar ne daga tsarin wutar lantarki mai amfani da hasken rana da shirin samar da mita da dai sauran su. Minisatan ya bayyana hakan ne lokacin taron masu ruwa da tsaki wanda ya gudana a garin Jalingo da ke cikin Jihar Taraba.

Da ya ke gabatar da jawabi ga matasa, Mamman ya bukaci matasan su zauna lafiya, domin gwamnatin tarayya za ta cika musu bukatocinsu wajen samar da guraban ayyukan yi ga duk matasan Nijeriya a bangaren wutar lantarki ta hanyar shirin samun wutar lantarki daga hasken rana guda miliyan biyar. Ministan ya yaba wa matasan wajen bayyana abubuwan da ke ci musu tuwo a kwarya. Ya bukaci matasan su guji gudanar da zanga-zangar tashin hankali a dai-dai lokacin da shugaban kasa ya ke shirin aiwatar da cika musu bukatocinsu da kuma ayyukan inganta rayuwar matasan kasar nan.
“Akwai shirin da za a aiwatar wanda zai tabbatar da ganin mafi yawan matasan Nijeriya sun sami ayyukan yi. Wannan yana daya daga cikin wani bangare na kwamitin shugaban kasa Muhammadu Buhari na tsamo mutane miliyan 100 daga cikin kangin talauci a shekaru 10.
“Daga cikin wadanda za su amfana da shirin wanda na samu, matasa ne za su amfana da dukkanin bangaren makamashin. Wannan wata hanya ce da gwamnatin tarayya za ta inganta rayuwar matasan Nijeriya da kuma ayyukan kulawa da mita da kamfanoni ke yi.”

Exit mobile version