Gwamnatin Abiya Za Ta Fara Hukunta Masu Watsar Da Bola A Ko’ina

Gwamnatin jihar Abiya ta ce; za ta fara hukunta masu zubar da bola a ko’ina musamman ma masu ba da hayar gidajensuda masu hayar suna kuma zubar da bola a ko’ina a kofar gidajen na su.

Gwamnan jihar, Okezie Ikpeazu shi ne ya bayyana hakan a birnin tarayya Abuja a jiya Lahadi, inda ya gargadi musamman mazauna Aba, cibiyar kasuwanci na jihar, na yadda suke kawo wa gwamnatin jihar cikas akan shirinta na tsaftace jihar. Ya ce; masu barin bola a kofar gidajensu suna watsarwa ko’ina, kamar suna gayyatar ambaliyar ruwa ne. Ya ce; lokaci ya yi da mutane ya kamata su sani cewa akwai gudummawar da za su bayar wajen taimakon gwamnati domin ta kawo karshen zubar da bola a ko’ina.

Exit mobile version