Gwamnatin Adamawa Ta Dakatar Da Ayyukan Mafarauta A Jihar

Daga Sulaiman Ibrahim,

Gwamnatin Adamawa ta haramta ayyukan kungiyar kwararrun mafarauta ta Nijeriya a fadin kananan hukumomi 21 na jihar.

Matakin na kunshe ne cikin wata sanarwa da Mista Humwashi Wonosikou, sakataren yada labaran gwamna Ahmadu Fintiri ya fitar a Yola.

A cewar sanarwar, Fintiri ya haramta kungiyar ne biyo bayan rahotannin cin zarafi da kuma barazanar tsaro daga mafarautan.

Fintiri ya ce abubuwan da suka faru kwanan nan a kananan hukumomin Demsa, Numan, Lamurde, Guyuk da Shelleng su suka tilastawa gwamnatin daukar matakin gaggawan.

Exit mobile version