Connect with us

KASASHEN WAJE

Gwamnatin Amurka Za Ta Hana Amfani Da Manhajar ‘Tik-Tok’ A Kasar

Published

on

Shugaban Kasar Amurka Donald Trump ya ce yana gab da ya haramta amfani da manhajar dandalin TikTok.Ya shaida wa manema labarai cewa zai saka hannu kan wata dokar bangaren zartaswa a yau Asabar.

Jami’an tsaron Amurka suna zargin cewa za a iya amfani da Tik-Tok, wadda kamfanin ByteDance na China ya mallaka, wurin satar bayanan sirri na Amurkawa.

TikTok ya karyata wannan zargin na cewa gwamnatin China ce ke iko da shi kuma ba ya bai wa gwamnatin bayanan masu tahamulli da shi.

Dandalin wanda ake dauka tare da yada gajerun hotonan bidiyo, na da masu amfani da shi kusan miliyan 80 a kasar Amurka kuma rufe shi ba karamar asara ba ce ga kamfanin.

“Za mu toshe Tik-Tok a Amurka” in ji Trump.
Advertisement

labarai