An bayyana cewar gwamnatin APC mai ikirarin samar da tsaro, lafiya, yaki da cin hanci da rashawa hadi da farfado da tattalin arzikin Nijeriya da cewar ta kasa-kasau wajen samar wa jama’an kasar Nijeriya da jihar Bauchi ci gaba.
Alhaji Gambo Abdullahi Bababa shugaban masu tsaftace maganin gargajiya na jihar Bauchi shi ne ya shaida hakan a hirarsa da wakilinmu a Bauchi, ya kara da cewa a matsayinsu na wadanda suke kallon siyasa, sun sha mamakin yadda gwamnatin APC ta gaza samar wa jama’an Nijeriya ababen more rayuwa, a maimakon hakan ma jefa jama’a cikin fatara da yunwa ta kara yi.
Yake cewa, “gaskiya yadda muka tsammaci shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yi wajen samar wa ‘yan Nijeriya saukin rayuwa gaskiya ba haka muka tarar ba, domin a yanzu sai dai mutum ya ki fada maka gaskiya ana cikin matsanancin yanayin rayuwa, malam ka tashi ka shiga cikin jama’a ka bincike yadda suke rayuwa sai ka tausaya.
“yaushe ne gyaran zai samu a Nijeriya ana fama da yunwa ko sai jama’a sun fara mutuwa?, shekara uku jama’a suna kuka haba! Gwamnatin Buhari ta ce za ta yaki zalumci da matsalar tsaro, yau muna gani Janaral na soja aka sace aka hallaka ina mu ga talakawa? Don haka babu wani maganar tsaro da aka samu a kasar nan; ga Zamfara da sauran wurare matsalar tsaro na ci gaba da aukuwa sai mu ki fadin gaskiya mu ce an samu tsaro gaskiya Buhari idan zai tashi ya yi gyara ya tashi, idan ba zai tashi ba kuma jama’a mu nema wa kanmu mafita a zaben 2019,” Inji shi
Ya shaida cewar dole ne Buhari ya sake lale hadi da tashi tsaye domin ganin rayuwar jama’an Nijeriya ta ingata, ya kuma tabo batun adalci da APC ke batu, inda ya shaida cewar a zaben fidda gwani da jam’iyyar ta yi sun tabbatar da jam’iyyar ba adalci ta sanya a gaba ba, ya yi zargin cewar a wurare daban a jihar da yake ta Bauchi ba a gudanar da zaben amma sai aka ce ga sakamako, “nadi ne kawai APC ta yi, bai dace jam’iyyar da ke ikirarin adalci ta tafka hakan ba,” Inji shi
Gambo Bababa da ya juya kan jihar Bauchi kuwa, ya shaida cewar gwamnan jihar ya bar jama’a cikin kuncin rayuwa, “Jihar Bauchi kam ai sai dai mu nemi tsira daga Allah, domin gwamman gwamnatin ta APC ta durkusar da komai, idan ka shiga kasuwar ‘yan kasuwa ba walwala, ma’aikata basa jin dadi, babu kudade a hanun jama’a don Allah yaushe ne ci gaban zai zo.
“da wannan gwamnatin na APC a jihar Bauchi wallahi gara gwamnatocin da suka shude, don haka ni ina kira ga gwamnan jihar Bauchi ya sani jama’a suna bukatar canji idan bai canza ba a dan wannan lokacin ‘yan Bauchi fa za su canza, don haka ina ganin ya dace a tashi tsaye wajen samar wa jama’a ababen da zai kaisu ga jin dadin gwamna,” Inji Gambo Bababa.