Daga Khalid Idris Doya,
Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed ya nuna takaicinsa na cewar, duk da makudan kudade da gwamnatin jihar take kashewa na fiye da naira biliyan guda a kowane wata kan kiwon lafiya tun daga tushe, ma’aikatan kiwon lafiya a karkashin wannan shiri ba su zuwa wuraren ayyukan su a cibiyoyin kiwon lafiya daban-daban da suke fadin jihar.
Ya fahimci cewar, ma’aikatan sa kai kan lamuran kiwon lafiya su ne ala-kulli halin suke bakin ayyuka, ba ainihin ma’aikata ba, dalilin da ya sa kenan gwamnati take fafitikar neman kudade domin daukar wadannan ma’aikatan wucin-gadi ko nasa kai.
Gwamnan yana jawabi ne a wata cibiyar kiwon lafiya dake cikin garin Azare, yayin da yake cigaba da buda ayyukan cigaba dake sassan jihar Bauchi, inda yake cewar, gwamnati za ta yi amfani da ‘yan kudade dake raritar ta domin tura wadannan ma’aikatan sa kai zuwa makarantar koyon ayyukan kiwon lafiya, domin samun cancantar daukar su aiki a cikin gwamnati.
Ya ce, “Ina matukar farin ciki da yadda wadannan ma’aikatan sa kai suke gudanar da ayyuka a cibiyoyin kiwon lafiya, a yayin da ainihin ma’aikata suke yin sakaci da ayyukan su. Don haka nake jan hankali wadannan ma’aikata na wucin-gadi da su cigaba da gudanar da ayyuka, tare da basu tabbacin cewar, bada jimawa ba, za mu dauke su aiki na dindindin.”
Sanata Bala Mohammed ya kuma ba su tabbacin cewar, gwamnati za ta yi dukkan mai yiwuwa domin samun rarar kudade da zai bada damar daukar su ayyukan gwamnati na din-din-din, yana mai cewar, “Mun tafi sarmadan akan wannan niyya domin cimma manufar samar da ayyukan yi wa wadannan ma’aikata masu kishin jiha”.
Ya kuma kara tabbatar wa wadannan ma’aikatan kiwon lafiya da cewar, “Bada jimawa ba, za mu daidata muku tsarin albasu a cikin ayyukan gwamnati, domin a halin yanzu muna nan muna share ma’aikatan bogi dake hana ruwa gudu. Kuma muna nan kan wannan fafitika na share ma’aikatan bogi cikin kankanin lokaci, biyo bayan wani kwamiti da muka kafa karkashin jagorancin Mukaddashin gwamnan jiha, Sanata Baba Tela.
Dangane da wannan manufa ce, gwamnan ya umarci kwamishinan lafiya na jihar domin ya yi kididdigar yawan wadannan ma’aikata nasa kai da zumma share masu fagen zuwa makarantar koyon aikin likitanci kan hanyar su ta zamowa sahihan ma’aikatan gwamnatin jihar Bauchi.
A gefe guda, gwamnan ya bayyana cewar gwamnatinsa ta samu nasarar sake kudaden hadaka da kungiyoyin tallafi wanda hakan ya bada damar samar da manyan da kananan asibitocin kula da lafiya a fadin jihar, tare da maida hankali wajen biyan kudaden hadaka a fannoni kula da lafiyar yara da Mata domin rage yawaitar mace-macen jarirai a lokacin haihuwa.