Gwamnan jihar Bala Bala Muhammad ya bada tallafin naira miliyan daya ga iyalan wata karamar yarinya ‘yar shekara shida wacce wasu marasa imani suka yanke mata al’auranta a jihar Bauchi domin fara mata jinya a asibitin koyarwa ta Malam Aminu Kano (AKTH), da ke jihar Kano.
Idan za ku iya tunawa dai mun baku labarin da ke cewa ‘yan sanda sun kama wani matashi dan shekara 20 mai suna Adamu Abdul Ra’uf bisa zargin yanke al’aurar wata ‘yar shekara shida mai suna Safara’u Muhammad da ke karamar hukumar Jama’are, lamarin da ya sosa zukatan jama’a tare da tir da lamarin.
Gwamna Bala ya bada kudin ne a asibitin AKTB ga majinyaciyar ta hannun kwamishinan kananan hukumomi, Hon. Abdulrazak Nuhu Zaki wanda ya jagoranci tawagar da suka wakilci gwamna Bala Muhammad wajen zuwa asibitin domin duba lafiyar yarinyar tare da nuna alhininsa kan wannan ta’asar.
Bala Muhammad ya yi tir da Allah wadai da lamarin, ya na mai cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci irin wannan danyen aikin ba kuma za su tabbatar an zakulo hakikanin wadanda suka dauki nauyin wannan aika-aikatar domin hukunta su.
Gwamnan ya jajanta tare da nuna kaduwarsa kan lamarin, ya na mai bada tabbacin gwamnatin jihar na yin duk mai yiyuwa domin tabbatar da adalci ga yarin da aka yi wa wannan mummunar aika-aikar.
Gwamnan ya kuma sha alwashin cewa gwamnatin jihar za ta kula da dukkanin jinyar yarinyar har zuwa warkewarta.
Baya ga kudin, tawagar sun kuma bada tallafin kayan abinci ga iyalan yarinyar, “Gwamnatin Bauchi za ta dauki nauyin jinyar yarinyar nan har zuwa warkewarta,” inji shi.
Ita ma da ta ke nata jawabin, kwamishinan mata na jihar Hon. Hajara Jibrin Gidado wacce ta wakilci matar gwamnan jihar Aisha Bala, ta ce, tunin ofishinta ya fara tuntubar manyan Lauyoyi domin ganin an dauki matakin shari’a kan wadanda suka lalata ma yarinyar rayuwarta.
Iyalan yarinyar sun nuna godiyarsu a bisa nuna damuwa da gwamnatin jihar ta yi.
Dakta Mahmud Kawu Magashi, wanda ya yi bayanin halin da a ke ciki ga tawagar, ya tabbatar da cewa likitoci da dama sun maida hankali wajen ganin sun taimaki yarinyar.
Aniyar Ganduje Ce Ta Haifar Da Ingantaccen Zabe A Kano – Yusif Ali
Daga Abdullahi Muhammad Sheka, An bayyana cewa, kyakkyawar aniyar Gwamna...