Gwamnatin Bauchi Ta Haramta Sana’ar Acaba A Babban Birnin Jihar

Za Ta Kawar Da ‘Yan Kasuwan Da Suka Mamaye Wuri Ba Bisa ka’ida Ba

Daga Khalid Idris Doya, Bauchi

kasa da shekara guda da sanya hannu kan dokar kafa hukumar kula da cinkson ababen hawa a Jihar Bauchi (BAROTA), wanda Gwamna Bala Muhammad ya yi, hukumar a yanzu haka ta shelanta shirinta na tilasta bin dokar haramta Acaba a cikin garin Bauchi.

Shugaban hukumar, Air Commodore Tijjani Baba Gamawa (Mai ritaya) shi ne ya shaida hakan a wani taron manema labarai da ya gudanar a Bauchi jiya, yana mai cewa daga yau duk wani dan Acaba da aka kama shi a cikin kwayar Bauchi na sana’ar Acaba to lallai za a kamasa kuma zai fuskanci fushin hukumar.

Gamawa ya bayyana cewar sun gano wadanda suke gudanar da harkokin kasuwanci ba bisa ka’ida ba wadanda suka mamaye wuraren da aka tanadar domin wasu muhimman abubuwa su 298 a kasuwar Central da ke cikin garin Bauchi, don haka ne ya ce sun dagesu daga wannan wajen tare da samar musu da wani wurin a harabar ofishin ma’aikatar Aiyuka inda za a baiwa kowanne fili mai murabba’in mita 3 da 4, tare da basu wa’adin watanni uku su gina shagunan su na kasuwanci.

Alhaji Tijjani Gamawa ya yi bayanin cewa wadanda suke kasuwanci ba bisa ka’idar ba sun rufe dukkanin mashigar kasuwar Santaral tare kuma da toshe hanyoyin da suke cikin kasuwa gami da cinkushe wuraren ajiye ababen hawa a bisa gudanar da kasuwancin da suke yi ba bisa ka’ida ba.

Sannan kuma, shugaban hukumar ya bayyana cewar masu sana’ar Kabu-kabu da Keke-Napep daga yanzu an hanasu yin goyon mataimakin direba ko direban wucin gadi a cikin Keke Mai kafa uku, “Wani sara da masu keke-napep ke yi shine goyon direban wucin gadi wanda in matuki ya gaji shi ma zai dauka ya ci gaba da ja, wani lokacin sai ka ga matukin keke amma akwai direbobi biyu da suke gefensa wai safiya ba za mu lamunci hakan ba.

“Mun dauki matakin hana goyon direban sakamakon matsalolin da aka fuskanta na tsaro, inda za ka ga matukin keke napep ya goyi direbobinsa biyu a wani lokaci suna kwace wa mata jakuna da sauran ‘yan matsalolin da aka gano,” a fadinsa.

Har-ila-yau, ya kuma bayyana cewar masu ajiye ababen hawa a kan hanyoyin ko masu kwasan fasinjoji a bakin hanyoyi dukkaninsu an hanasu hakan tare da daukan matakan tilasta musu bin umarnin kwamitin tilasta bin ka’idojin amfani da hanya na kiyaye cinkoson ababen hawa.

“A yau muna son mu shaida muku cewa kwamitin hana cinkoson ababen hawa da sauke fasinja a kan hanya ya yi kokarinnsa, saboda sama da wata uku da suka wuce ta kawo tsarin a cikin birnin Bauchi wanda aka tsarkake masu daukan fasinja da ajewa ba bisa ka’ida ba, inda aka maidasu zuwa wuraren da gwamnati ta ware tare da amincewa domin hakan.”
Ya kuma ce kwamitin tilasta bin ka’idoji ya kuma wayar da kan jama’a dangane da jigilan fasinjoji ba bisa ka’ida wanda tunin aka samu sauyi sosai kan hakan kuma an baiwa hukumomin tsaro umarnin tabbatar da wannan, ya kara da cewa, “Dokar haramta Acaba har yanzu yana nan daram dam a Bauchi, dokar tana nan kuma za mu cigaba da dabbaka wannan dokar nan take.”
Commodore Tijjani Gamawa ya kuma sake nanata cewa direban wucin gadi na Keke-napep ba za su bari a ci gaba da yin hakan ba don haka daga hanzu direba daya ne zai ke tuka keke-napep a yayin da ke kabu-kabun na sana’arsa.

Ya kuma nuna damuwarsa bisa ga yadda wasu ‘yan kabu-kabun adadaita sahu suke fitowa daga jihar Yobe zuwa Bauchi ba tare da bin ka’idojin da suka dace ba, yana mai cewa dukkanin wanda ke son yin sana’ar kabu-kabu na adaidaita sahu dole yayi rijista da hukuma domin tantancewa da kiyeye matakan tsaro.
“Dukkanin abubuwan da muke yi din nan muna yi ne saboda batu na tsaro, kuna sake da cewa Bauchi ce kadai jihar da ke cin gajiyar zaman lafiya da kwanciyar hankali a Arewa Maso Gabas don haka ba za mu nade hannayenmu mu bari wasu su kawo mana matsalar tsaro a jiharmu ba,” inji Gamawa.

Exit mobile version