Daga Khalid Idris Doya,
Gwamnatin Jihar Bauchi ta kafa wani kwamiti mai karfin gaske da zai tabbatar da shawo kan dukkanin wasu matsalolin da suke akwai a sashin biyan albashi da na fansho a jihar.
Wannan matakin na zuwa ne bayan wata ganawar sama da awa uku da suka gudanar a tsakanin gwamnatin jihar da kungiyoyin ‘yan kwadago da ke jihar, wanda gwamnan jihar, Bala Muhammad ya jagoranta.
Da ya ke bayani wa ‘yan jarida matsayar da aka cimma bayan ganawar, Shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin jihar, Dakta Ladan Salihu, ya yi bayanin cewa wannan matakin na nuna yadda gwamnan jihar Bala Muhammad ya himmatu wajen ganin an shawo kan dukkanin matsalolin da suke fuskantar sashin biyan albashin ma’aikata domin baiwa ma’aikatan karsashin gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.
“Ina cike da farin cikin sanar da ku da al’umman jihar Bauchi baki daya cewa dukkanin batutuwan da kungiyar kwadago ta baje a yayin zaman mun tattauna kuma an samu cimma matsaya masu nagarta a kansu.”
Ya bada tabbacin cewa, gwamnati mai ci a jihar za ta cigaba da yin aiki tare da kungiyoyin kwadago domin tabbatar da kyautata rayuwar ma’aikatan jihar a kowani lokaci, tare da yin aiki da su wajen ganin an shawo kan matsalolin da suke fuskantar sashin biyan albashi gami da dakile masu ci da gumin wasu.
“Idan kuka kalli irin muhimman mutanen da gwamnan ya sanya cikin kwamitin, za ku amince kan yadda shi gwamnan ya maida hankali wajen magance matsalolin da suke shafan biyan albashi da fansho nan take,” Ladan ya fada.
Ladan ya ce, akwai muhimmin batu da ya dace jama’a su lura da shi, “Ya kamata a gane mu a nan Bauchi ana biyan albashi kowace wata, a daidai gabar da ake kokarin dakilewa da tushe kafar sata a tsarin biyan albashi ne kuma wasu daga cikin ma’aikata ke samun ‘yan matsala nan da can. don haka daga yanzu an dauki matakan da kowani ma’aikaci ba zai sake kuka da matsalar albashi ba.”
Shi ma a fasa fannin, shugaban kungiyar kwadago ta kasa reshen jihar Bauchi (NLC), Kwamared Danjuma Saleh, ya ce a bisa kyawawan tattaunawa da suka yi a tsakaninsu da gwamnatin jihar, su na da tunanin janye yajin aikin da ake harsashen yinsa a jihar.
“Kamar yadda kuke gani, gwamnan jihar Bala Muhammad da kansa ya jagoranci ganawa a tsakanin gwamnati da kungiyoyin kwadago wanda muna cike da farin cikin domin an himmatu wajen shawo kan dukkanin matsalolin da muka nusar.”
Kwamitin wanda mataimakin gwamnan jihar Baba Tela zai jagoranta, yayin da kuma sakataren gwamnatin jihar Alhaji Muhammad Sabi’u Baba zai kasance sakataren kungiyar.
Mambobin kwamitin kuma sun hada da shugaban NLC a jihar da na TUC, gami kuma da NJC.
Sauran mambobin Shugaban ma’aikatan jihar Alhaji Aliyu Jibo, Babban mai baiwa gwamnan shawara kan harkokin ma’aikata, Mista Abdon Dalla Gin, Shugaban NULGE a jihar, tare da hukumomin da lamarin ya shafa a matsayin mambobi.
An baiwa Kwamitin wa’adin mako hudu da su kammala aikinsu tare da gabatar da rahoton aikin ga Gwamnatin jihar, an kuma kafa ne da zimmar shawo kan kalubale da matsalolin da suke fuskantar sashin biyan albashi da fansho a jihar.