Connect with us

RIGAR 'YANCI

Gwamnatin Bauchi Ta Nemi Afuwar Ma’aikatan Da Su Ka Fuskanci Jinkirin Albashi

Published

on

Gwamnatin jiha ta bayyana cewa babu wani cikakken ma’aikaci a jiha da ba ta biya shi albashin sa na watan Yuli ba, ta kara da cewa sama da kaso sittin na ma’aikatan ta sun samu albashin su tun kafin sallah.

Da ya ke zantawa da manema labarai a gidan gwamnati, kwamishinan kasafi da tsare tsare Dakta Aminu Gamawa ya bayyana cewa tsaikon da aka samu matsaloli ne daga bankuna.
Duk da haka dai ya nemi afuwa da gafarar ma’aikatan da jinkirin ya taba wa walwala da jin dadi, inda ya ke bada bayanin cewar Gwamnatin a shirye take wajen ganin ta kyautata wa ma’aikatan ta da kuma faranta musu a kowani lokaci.
Kwaminshinan ya yi watsi da zargin cewa ba a biya wasu ma’aikata albashin su ba, ya jaddada cewa gwamnatin jihar za ta biya kowane ma’aikaci da ya cika sharudda hakkinsa.
Dakta Gamawa a madadin gwamnatin jihar ta Bauchi sai ya yi amfani da damar wajen rarrashin wadanda tsaikon ya shafa tare da neman afuwarsu, yana mai bada tabbacin cewa za a samu gyara kan lamarin ta yanda ma’aikatan ba za su ke jigata sakamakon jinkirin zuwan albashinsu ba.
Kwamishinan ya ce gwamnatin Bauchi ta dade tana biyan albashin ma’aikatan ta ba tare da tangarda ba, wanda ya sha alwashin ci gaba da hakan daga Gwamnatin jihar.
A cewarsa, tun farkon darewar ta kan karamar mulkin jihar, gwamnatin Sanata Bala Muhammad ta ke bada fifiko ga biyan albashi da kuma fansho kana ya ce za a ci gaba da biya cikin yardar Allah.
Kwaminshinan ya ce gwamnatin jihar ta sake bullo da sabbin dabarun cire ma’aikatan bogi daga cikin tsarin biyan albashi.
Idan za ku iya tunawa dai wasu ma’aikatan jihar sun yi korafin yin babban sallah cikin yanayi marar kyawu sakamakon rashin shigar albashinsu. Tun watan June dai wasu ma’aikatan jihar ke korafi kan albashi kama daga wadanda aka yanke musu kaso daga albashi sai masu kukan rashin samun albashin ma gaba daya. Sai dai Gwamnatin ta ce gyara take yi komai ya kusa zama tarihi tare da baiwa ma’aikatan hakuri bisa tsaikon.
Advertisement

labarai