Daga Khalid Idris Doya, Bauchi
Gwamnatin Jihar Bauchi karkashin gwamnan jihar Muhammadu Abdullahi Abubakar ta fara rabon magangunan zazzabin cizon sauro, gidajen sauro da kuma kayayyakin gwaje-gwajen zazzabin cizon sauron ga cibiyoyin kiwon lafiya guda 100 da suke fadin kananan hukumomi 20 na Jihar Bauchi.
Rabon kayan wanda ya gudana a karkashin hukumar BACATMA da hadin guiwar babban bakin duniya na shirin ceto rayukan mutune miliyan guda a jihar.
Da yake yi wa LEADERSHIP A Yau karin bayani kan rabon, babban Sakatare a hukumar yaki da zazzabin cizon sauro, tarin fuka, cuta mai karya garkuwar jiki na jihar Bauchi (BACATMA), Dakta Masur Mustapha Dada ya bayyana cewar a ranar Litinin din da ta gabata ne suka kaddamar da fara rabon kayyakin zazzabin cizon sauron da magungunan domin kare lafiyan al’umman Jihar Bauchi.
Dakta Dada ya cigaba da bayyana cewa a kowace karamar hukuma sun zabi asibitoci guda biyar ne, inda asibiti kwara daya cur ne a dukkanin fadin kananan hukumomin jihar Bauchi 20 da ake da su “Yanzu haka ana ci gaba da rabon wannan maganan a fadin jihar, kuma ana raba su kyauta ne, idan mutum ya zo asibiti yana zazzabi za a basa magani kyauta ne, gwajin da za a yi maka kyauta ne, kuma idan aka tabbatar mutum yana da zazzabin cizon sauro shi ma kyauta muke baiwa mutum maganin”. Inji Daktan Dada
Daktan ya ce, shi kuma gidan sauro ba kowa da kowa suke rabawa ba sai wanda ya cancanta “Shi gidan sauro ba kowa da kowa ake bayarwa ba, akwai yara y’an kasa da shekara daya ana basu gidan sauro daya, matan da suke cikin shekarun haihuwa suma ana basu, da zarar ta fara zuwa awo a wannan lokacin zamu dauki kwara daya mu bata. Yanzu haka kowani mataniti mun basu gidajen sauro biyu-biyu”.