Khalid Idris Doya">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home LABARAI

Gwamnatin Bauchi Ta Raba Keke-Napep 1,000 Don Bunkasa Zirga-zirga

by Khalid Idris Doya
December 6, 2020
in LABARAI
2 min read
Gwamnatin Bauchi Ta Raba Keke-Napep 1,000 Don Bunkasa Zirga-zirga
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Muhammad ya kaddamar da rabon Keke-Napep guda dari shida da hamsin da biyar (655) tare da motocin Kabu-kabu guda 154 domin bunkasa lamuran sufuri da zirga-zirga a fadin jihar.
Idan za ku iya tunawa dai, gwamnan a zango na farko ya rabar da kekunan sana’a mai kafa uku (Keke-napep) sama da dari uku da arba’in da biyar 345 wanda a bisa rabon da aka yi a wannan lokacin ya kawo adadin kekuna guda 1,000 da gwamnan ya rabar a matsayin rance ga wadanda ba su da ayyukan yi
Da ya ke jawabinsa a yayin taron, gwamnan jihar Bala Muhammad ya nuna cewa sun samar da tsare-tsare masu sauki da za su taimaka wa matasa sosai, don haka ne ya nemi hadin kansu wajen ganin an cimma nasarar kyautata musu rayuwa.
Ya shaida cewar rabon motocin a daidaita sahu da na Kabu-kabun na daga cikin yunkurin gwamnatinsa na cika alkawuran da ta dauka wa jama’a ne ta fuskacin inganta musu tattalin arzikinsu don ba su damar tsayuwa da kafafunsu.
A cewarsa, tunanin hakan ya biyo bayan nazarin hanyoyin da za su bi wajen fidda jama’a daga cikin takauci ne da fatara.
A cewar gwamnan shirin sayo Keke-Napep da motocin Kabu-kabun na gudana ne a karkashin shirin kyautatawa da samar da ayyukan dogaro da kai ta ‘Kaura Economic Empowerment Programme’ (KEEP 2020).
A yayin da ya ke kaddamar da rabon ga wadanda suka ci gajiyar, Gwamna Bala Muhammad ya shaida cewar nan gaba rabon kashi na uku ma zai gudana, ya na mai cewa sun gama shirin rabon rance ga ‘yan kasuwa domin bunkasa musu harkokin kasuwancinsu.
A cewarsa, rabon kudin rancen zai tafi ne ta hannun shugabanin ‘yan kasuwa wanda za a raba karkashin ma’aikatar da ke kula da harkokin kasuwanci da masana’antu tare da tsara yanda wadanda suka ci gajiyar za su biya cikin sauki domin a sake bai ma wasu su ma don su mora.
“Yanzu haka wannan ma’aikatar tana tattaro kudaden da gwamnatin baya ta rabar domin kara baiwa wasu don su ma ci gajiyar rancen.”
A cewarsa samar da tsare-tsaren sun zama musu dole ne domin ganin an shawo kan matsalar rashin ayyukan yi da inganta kasuwanci a fadin jihar musamman ga matasa.
Bala ya kara da cewa, tun da gwamnati ba za ta iya daukan kowa da kowa a aiki ba, akwai bukatar su karfafi masu sana’o’in kashin kai domin fadadawa don ganin matasa da dama sun samu guraben ayyuka a karkashinsu.

SendShareTweetShare
Previous Post

Gombe Ta Bada Kwangilar Aikin Kwarin Jami’ar Jihar GSU Zuwa Malam Inna Kan Kudi Biliyan N2.9

Next Post

An Karrama Kungiyar Noman Masara Da Sarrafa Ta Reshen Jihar Katsina

RelatedPosts

Sojoji

Tsofaffin Sojoji Sun Nemi Karin Kudin Fansho

by Khalid Idris Doya
9 mins ago
0

Kungiyar tsofaffin sojoji ta kasa reshen jihar Anambra ta bukaci...

Ali Baba

Zaben Kananan Hukumomi: PDP Kwankwasiyya Ta Maka KASEIC A Kotu

by Khalid Idris Doya
25 mins ago
0

Bangaren Kwankwasiyya na jam'iyyar PDP a jihar Kano, ta jadadda...

Kurkuku

Binne ‘Ya Da Rai: Kotu Ta Yankewa Uba Hukuncin Kisa

by Khalid Idris Doya
34 mins ago
0

Babbar Kotun jihar Jigawa, da ke  garin Ringim ta yanke...

Next Post
AFAN Ta Soki Amince Wa Kamfanoni Hudu Shigo Da Masara Nijeriya

An Karrama Kungiyar Noman Masara Da Sarrafa Ta Reshen Jihar Katsina

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version