Connect with us

LABARAI

Gwamnatin Bauchi Ta Shirya Bunkasa Ruwa Da Muhalli

Published

on

Gwamnatin Jihar Bauchi ta fitar da naira dubu 700,000 na hadaka domin samar da ruwa mai tsafta hadi da tsaftar muhalli a jihar, mai rikon mukamin gwamnan jihar kuma mataimakin jihar, Arc. Abdu Sule Katagum shi ne ya shaida hakan.

Mai rikon mukamin gwamnan ya yi bayanin cewa, tuni gwamnatin jihar ta fitar da naira dubu N350, 000 domin fara aiwatar da shirin, yana mai kara wa da cewa, sauran naira dubu N350, 000 gwamnatin za ta fitar nan bada jimawa ba domin samun nasarar shirin na tsaftace ruwa da na muhalli a jihar

Arc. Abdu Sule Katagum wanda ke jawabi a lokacin da tawagar wakilai asusun tallafa wa kananan yara na majalisar dinkin duniya UNICEF suka kawo masa ziyara a ofishinsa da ke Bauchi.

Ya shaida cewar gwamnatin jihar ta himmatu wajen tabbatar da tsaftar ruwa da na muhalli a fadin jihar ta Bauchi domin kyautata rayuwar jama’an jihar, ya kuma bayyana cewar sun bayar da goyon baya dari bisa dari wa shiri.

Katagum ya jinjina wa UNICEF a bisa tallafi daban-daban da suka shafi sha’anin lafiya, ilimi, ci gaban yara da sauran shirye-shiryen da suke da alaka da harkar lafiya a jihar.

Babban sakataren (RUWASSA), Engr. Garba Babaji Magaji ya shaida cewar tun fara aiwatar da shirin WASH a shekarar 2010 an fara ne da kananan hukumomi uku inda aka fadada shirin zuwa kananan hukumomi 12 da suke jihar, biyu bayan nasarorin da ake samu ta cikin shirin.

Magaji ya ce a shekarar 2011 mutane miliyan biyu suka samu ruwa a karkashin sa’ayin shirin WASH.

Da yake maida jawabi jagarin shirin WASH, Mr. Zaid Jurji  ya bayyana cewar gwamnatin jihar Bauchi ta himmatu wajen mara wa shirin baya don ganin ya kai nasara, musamman yadda gwamnatin ta mara baya wa shirin a 2018.

Jurji ya yi bayanin cewar jihar Bauchi ta yi sa’ar samun kanta daga cikin jahohin da suka fi samun tallafin shirin a fadin kasar nan, ya bayyana cewar hakan zai bayar da dama a samu dumbin masu cin gajiyar shirin a Bauchi.
Advertisement

labarai