Gwamnatin Bauchi Ta Yi Jarabawar Karin Girma Ga Ma’aikata Dubu 1,527

Daga Khalid Idris Doya, Bauchi

Gwamnatin jihar Bauchi ta fara gudanar da jarabawar karin girma wa ma’aikatan gwamnati su dubu daya da dari biyar da kuma ashirin da bakwai 1,527 na shekara ta 2017, wanda aka fara fafata jarabawar a ranar larabar da ta gabata. Jarabawar dai zata ba, ma’aikatan damar daukaka musu darajar mukamansu daga mataki zuwa matakin gaba da matakin da yake.

A jawabinsa na bude taron jarabawar, shugaban ma’aikata na jihar Bauchi Alhaji Liman Bello ya bayyana cewar shirin karin girman na daga cikin manufar su ne na daukaka darajar hazikan kuma kwarrarun ma’aikatan gwamnati domin a kaisu zuwa matakin da ta dace domin aiki ya cigaba, da samuwa yadda ake da bukata kamar yadda yake a tsarin aiki.

A cewarsa babban manufar yin jarabawar wa ma’aikatan dai ita  ce, domin a kai wadanda suka cancanta zuwa matakin da ya dace,tare  da tabbatar da ma’aikatan gwamnati su na bin ka’idojin aiki, samar masu da kwarewa, da kuma samar musu da ilimin kimiyya wanda zai taimaka musu sosai wajen tabbatar da yin aiyukansu yanda ya dace.

Liman Bello ya bayyana cewar gwamnatin jihar mai ci ta ba da gaggarumar gudanmawa da himma sosai, wajen tabbatar da samar wa ma’aikatanta horo na cikin gida, da kuma horon kai aiyukansu a fannoni daban-daban, domin ganin an samu nasarar taimaka wa al’umma a ma’aikatu da kuma wuraren aiyukan da gwamnati ke yi, duk domin al’umman, har ila yau domin a tabbatar da samar da al’umma ta gari.

Shugaban ma’aikatan ya kuma bayyana cewar yadda ake gudanar da jarabawa da, kum horo wa ma’aikatan gwamnatin hanya ce, da za ta samar da kykkyawan yanayin cigaban al’umma da kuma kasa kana da kuma tabbatar da inganta su kansu, ma’aikatan gwamnatin wanda a cewarsa hakan zai kawo canji sosai a cikin sha’anin gudanarwa.

Liman Bello ya yi amfani da wannan damar wajen bitar, yin kira ga ma’aikatan gwamnati da cewar su tashi tsaye tare da  fargawa, domin je wa ma’aikatansu don aiwatar da dukkanin wani horo da kuma ilimin da suka samu a jarabawar gwajin da aka yi musu domin a samu kaiwa ga babban manufar inganta aiki da aka sanya a gaba.

A nasa jawabin, babban sakatare a ma’aikatar tabbatar da inganci aiki da kuma da’ar ma’aikata na jihar Bauchi Alhaji Sani Ahmed, wanda ya samu wakilcin Darakta a ma’aikatar Alhaji Tijjani Ishiyaka ya bayyana cewar abinda da suke fada samu a wajen ma’aikatar dai shine, aiwatar da dukkanin abin da suka samu daga horon jarabawar karin girman, ya bayyana cewar ba nufinsu a yi jarabawa a samu karin girma shi ke nan ba; ya bayyana cewar aiwatar da ayyukan a cikin ma’aikatu shine babban abinda da suke bukata daga wajen ma’aikatan da gwamnatin ta daukaka musu girma a wajen aikinsu.

Tun da fari Shugaban cibiyar bada horo na ma’aikatan ‘Dugge Management Serbice Limited’ Alhaji Gambo Magaji ya misalta taron jarabawar gwajin a matsayin matakin da zai fiddo ma’aikatan da suka cancanta da kuma sake nemo hazikan da za su jagoranci aiyukan gwamnati a sassan ma’aikatu tare da daukaka darajar aiki daga tsohon ya yi zuwa na zamani.

Magaji ya shawarci ma’aikatan da cewar su tabbatar sun tashi tsaye domin tafiyar da aiki daidai, da zamanin da suka samu kai a ciki ba wai tafiyar da aiki da ilimi tun fil .

Wakilinmu ya shaida mana cewar jarabawar da za a yi wa ma’aikatan dai zai biyo bayan horo kan dabarun inganta aiki ne, da kuma basu ilimin da ya dace kan fannoni daban-daban har guda goma wadanda dukkaninsu, suna tafiya ne da ilimin zamani da kuma ilimin inganta aiki a kowace marhala. Tuni dai ma’aikatan suka yi ta daukar darasi, ana sa ran  ma’aikata 1517 ne za  a yi musu karin girma daga ma’aikatu daban-daban na jihar Bauchi.

 

 

Exit mobile version