Daga Khalid Idris Doya, Bauchi
Sakataren Gwamnatin jihar Bauchi, Alhaji Nadada Umaru Zannan Misau ya jinjina wa wasu mata masu koyon sana’ar dogaro dai don tsayawa da kafafusnu ba tare da jiran sai an yi musu a rayuwa ba. A cewarsa mata su fito suna buga-bugan neman hanyoyin da za su dogara da kansu abin a yaba musu ne.
Sakataren Gwamnatin ya bayyana hakan ne a wata ziyarar da ya kai cibiyar koyon sana’o’in dogaro da kai na M.A Abubakar na wucin-gadi a makarantar Firimare na Kobi a ranar Laraban nan da ta gabata, inda ya bayana cewa gwamnati za taimaka masu.
Sakataren Gwamnatin ya ce wannan yunkurin da gwamnatin ke yi wajen tabbatar da mata da matasa sun samu tsayawa da kafafunsu a matsayin wani mataki na rage talauci a cikin al’umma. “Da amincewar gwamnan jihar Bauchi na zo domin na ga yadda kuke koyon sana’o’in naku, kuma ya tabbatar da cewar za a taimaka maku,” in ji shi.
Daga nan sai Nadada Umaru ya yi kira ga matasan da cewar su daure a akan sana’o’in da suke kai, ba biye wa kalle-kallen na wani ba, “abin da ke hana wasu ci gaba, sai sun fara sana’a, sai su kuma kalli wani ya yi kudi, sai su saki tasu sana’ar su dumfari na wanda suka leko. Wannan ba hali ba ne na kwarai,” ya ce.
Ya ci gaba da cewa, idan mata ba su iya samun yadda za su yi da rayuwarsu ba, to tabbas akwai matsala a jibge. “Gwamanatin jihar Bauchi za ta taimaka muku da kayan sana’o’i da jari, za mu kuma sanya ido ga mata idan an baki keken dinki kika sayar, don kanki,” In ji shi.
Tun da fari a nasa jawabin, Barista Umar Faruk Gwadabe, Shugaban Hukumar inganta rayuwar mata da matasa ta jihar Bauchi (BACYWORD), wanda cibiyar koyon sana’ar ke hannun ma’aikatarsa, ya bayyana cewar, “yara ne suka ga ya dace su tara mata su koya musu sana’a, muka shigo domin mu hada kai don inganta rayuwar matan, mun tallafa musu da wasu kayayyaki a farko, amma duk abubuwan da ka ga suke fitarwa su suke kirkirar kayansu, illa dai muna sanya ido kan lamarin.”
Ya ci gaba da cewa, “matan da suke koyon sana’o’i a nan suna da matukar yawa, kuma a unguwanni da daman gaske suna ta tururuwa zuwa nan don su koyi sana’a. Don haka gaskiya dole ne gwamnati ta shigo domin taimaka wa wadannan matan don su ma su dogara da kansu.”
Sadik Abdullahi, shi ne shugaban wannan cibiyar ta M.A ABUBAKAR EMPOWERMENT AND BOCATIONAL TRAINING INITIATIBE, ya bayyana cewar, “Mun kafa wannan cibiyar ne domin koya wa mata da matasa sana’o’in dogaro da kai. Wannan masana’anta mun fara ne da dalibai dubu biyu, yanzu haka muna da dalibai dubu 5.”
Wasu mata da suka bayyana sun shaida cewar sun zo wannan cibiyar ne domin su koyi sana’ar dogaro da kai. A cewarsu sun fahimci rayuwar nan ta yanzu zama ba nasu ba ne.
Wakilinmu ya labarta mana cewar a cibiyar ana koyar da dinki, hada takalma, hada man shafe-shafe, zagin gano, sabulai na wanka da wanki , Mayukan gashi da na shafawa, Dinkakkun Zannuwan gadaje, Takalma, Jakukkuna, abubuwan wuya na mata da sauransu. Haka kuma a cibiyar ana koyar da karatun Boko da na Addini.