Daga Muhammad Maitela, Maiduguri
Gwamnatin jihar Borno ta bayyana gina sabbin kananan makarantun firamari biyu na musamman domin marayu ‘yan asalin jihar, wadanda suka rasa mahaifan su ta dalilin rikicin Boko Haram da ya addabi yankin.
Wannan bayanin ya fito ne daga bakin kwamishinan ilimin jihar, Musa Kubo a lokacin da yake zantawa da manema labarai a babban birnin jihar, Maiduguri a sa’ilin da ya ziyarci kammala aikin daya daga cikin wadannan makarantun fake yankin Ngomeri – Barwee da kuma ta rukunin gidaje na 303 Maiduguri.
“Mun yi tunanin samar da wadannan makarantun ne domin bada cikakkiyar kulawa ga marayu wadanda matsalar Boko Haram ta raba su da mahaifan su. Bisa ga wannan ne gwamnatin jiha ta kuduri aniyar samar da wadannan makarantu na firamare na kwana hadi da kananan makarantun sakandari domin wannan manufa”.
Har wala yau, kwamishinan ya kara bayyana cewar gwamnatin jihar Borno ta gina wasu karin rukunin ajujuwa 16 fake cikin kwaryar Maiduguri a karkashin shirin ta na bunkasa makarantu, hadi da sake fasalin ilimin yara da manya zuwa ilimin boko da aka fi sani da ilimin zamani.
Alhaji Musa Kubo ya nusar da cewa baya ga wannan kuma, a cikin kokarin gwamnatin jihar Borno wajen bunkasa sha’anin ilimi, ta sake bunkasa gine-ginen makarantun jihar da tsarin ginin hawa daya mai dauke da ajujuwa 30 a cikin wakonnen su domin rage cunkoson dalibai a cikin manya da kananan makarantun jihar.
Yayin da ya ce, makarantun da suka samu irin gine-ginen sun kunshi ‘Government College Maiduguri’ da ‘Government Girls College Maiduguri’ kana da ‘Yerwa Gobernment Girls College’ sauran sune Government Day Secondary School, Zajeri; ‘Junior Secondary Schools’ ta Bulabulin, Ngomari da Bulunkutu, duk a cikin jihar Borno.
A wani batu na daban kuma, Kwamishina Kubo ya bayyana cewa, gwamnatin Borno ta kashe naira miliyan 200 million a ayyukan sannan da samar da na’ororin sadarwa a wasu makarantun jihar da suka hada da a Maiduguri, Kaga, Konduga da a karamar hukumar Jere.
Ya kuma nanata cewa Gwamna Kashem Shettima yayi rawar gani wajen sake ginawa da gyara makarantun da mayakan kungiyar Boko Haram ta barnata a jihar. Inda ya ce kawowa yanzu kikamin makarantu 22 aikin gyaran su ke gudana kuma akwai karin wasu makarantun a cikin garuruwan da al’ummun su suka koma da zama wadanda suma wannan aikin zai kai gare su. Inda ya nuna cewa kowacce daya daga cikin wadannan sabbin makarantu na marayu an tsara zata dauki dalibai 2, 000.
“Baki dayan makarantun kwana dake jihar Borno; wadanda a da aka garkame su, yanzu sun bude tare da ci gaba da daukar darussa kamar yadda aka saba. Sannan ina mai tabbatar maka cewa, a wannan shekara kadai gwamnatin jiha tana biyan naira miliyan 278, kudin daukar jarabawa ta kasa (National Examination Council and Senior School Examination Certificate) ga dalibai yan asalin jihar Borno”. Ya bayyana.
“Duk halin da muke ciki a yanzu alhamdulillah, yanayin tsaro ya inganta a jihar Borno. Amma a cikin wadannan shekaru da muka dauka, Boko Haram sun rusa rukunin ajujuwa sama da 15, 000 a makarantun mu dake kananan hukumomi 27 a jihar Borno baya ga daruruwan malamai da daliban da wadannan mayaka suka yi garkuwa dasu”. Inji kwamishinan.