Connect with us

RAHOTANNI

Gwamnatin Borno Ta Ware Naira Biliyan 1, Don Biyan Tsofaffin ma’aikata

Published

on

Gwamnatin jihar Borno ta ware Naira biliyan daya, domin fara biyan kudin sallamar tsofaffin ma’aikatan da suka yi ritaya a aikin gwamnati- garatuti.

Kudin wadanda wani bangare ne na kudaden da tsofaffin ma’aikatan da suka yi ritaya a aiki suke bin gwamnatin jihar, na kusan shekaru biyar, wadanda yawan su ya doshi Naira biliyan 20.

Bayanin haka yana kunshe a cikin wata sanarwar manema labarai, wadda shugaban ma’aikatan jihar Borno (Head of Serbice), Yerima Saleh, ya rattaba wa hannu, a Maiduguri, inda a ciki ya bayyana cewa, Gwamna Kashim Shettima ya bayar da umurnin ware kason farko, na Naira biliyan daya nan take, ga tsofaffin ma’aikatan.

Ya ce, kudin da ma’aikatan ke bi ya doshi naira biliyan 20, kuma hakan ya faru ne saboda yadda aka dauki shekaru biyar ba a biya su kudin ba- da suka kunshi ma’aikatu daban-daban tare da wasu hukumomi da cibiyoyi hadi da na kananan hukumomi 27, da ke aiki a karkashin gwamnatin jihar.

Bugu da kari kuma, ya bayyana cewa, gwamnatin jihar ta dage biyan kudaden tsufaffin ma’aikatan ne tun a cikin watan Yunin 2013, a lokacin da tattalin arzikin Nijeriya ya shiga watan yarajejeniya.

Malam Saleh ya ce, “gwamnatin jihar ta fara biyan wadannan tsufaffin ma’aikata wannan bangare na adadi na Naira biliyan daya”.

“Har wala yau kuma, daga cikin Naira biliyan daya, an shirya ware Naira miliyan 500 wajen biyan tsofaffin ma’aikatan jihar. Yayin da sauran Naira miliyan 500 kuma aka tsara kasa su gida biyu- tsakanin malaman firamari da na kananan hukumomi da suka yi ritayar”.

Haka zalika kuma ya shaidar da cewa, a haka gwamnatin za ta ci gaba da biyan tsufaffin ma’aikatan har ta biya Naira biliyan 20- na garatuti.

Dangane da hakan kuma, shugaban kungiyar kwadago ta kasa (NLC), reshen jihar Borno, Titus Ali Abana, ya bayyana cewa bashin kudin garatutin da tsofaffin ma’aikatan ke bin jihar sun zarta Naira biliyan 20.

Ya ce, daukar matakin biyan kudin sallamar ya zo ne bayan matakin da suka dauka na gudanar da yajin aiki.

Duk da wannan kuma, Mista Abana ya yaba da kokarin gwamna Kashim Shettima wajen bayar da umurnin fara biyan kudin, tare da bayyana cewa Naira biliyan daya sun yi kadan idan an kalli yawan kudin da tsufaffin ma’aikatan ke bin gwamnati.

Ya ce da farko kungiyar kwadago ta tsammaci cewa gwamnatin za ta bayar da umurni cire a kalla abin da bai gaza Naira biliyan 5 zuwa 10 ba- wajen fara biyan hakkokin.

Shugaban kungiyar ya nemi gwamnatin jihar ta dawo da tsohon tsarin cire Naira miliyan 150 a kowanne wata-domin biyan garatutin, wanda ta dakatar a shekarar 2013.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: