Muhammad Maitela" />

Gwamnatin Buhari Cikin Shekara Biyar: Nasarori Ko Tarin Matsaloli?

A daidai lokacin da gwamantin tarayya ta ayyana ranekun 29 ga watan Mayu, 12 ga watan Yuni a matsayin lokuta muhimmai a mulkin dimukuradiyyar Nijeriya, wadanda ma su madafun iko za  su yi  amfani da su  wajen  baje  kolin  manufofi tare da bahasin nasarori ko matsalolin  da  aka  samu ko  na kalubale a shekarar da ta shige.

A wannan jikon ne gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta ke cika shekaru biyar cur a karagar mulkin tarayyar Nijeriya, yayin da hakan ya jawo masu fashin baki da masana hadi  da  yan kasa  tofa  albarkacin bakin su dangane da nasarori ko akasin su da gwamnatin APC ta cimma.

Yan  kasar  da  dama  sun  fi karkata wajen alkawuran da shugaban kasa ya dauka a karkashin jam’iyyar APC, a lokutan yakin neman zabukan 2015 da na 2019.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da mataimakin shi, Farfesa Yemi Osinbajo da wasu jigajigan jam’iyyar sun yi wa yan Nijeriya alkawura sama da 100, da sharadin cewa matukar sun yi sa’ar dare madafun iko za su cika.

Ta hakan ne ya jawo yan Nijeriya za su so sanin ina aka kwana  dangane  da  wadancan alkawuran; an aiwatar da su ko yaya? Wanda ta janibin shugaban  kasa  Buhari  hadi da mukaraban sa, sun sha bayyana cewa sun kammala cika alkawuran da su ka dauka a wadancan lokuta.

A hannu guda kuma, yan Nijeriya da dama sun sha musanta zancen cika alkawuran da  aka  dauka  musu,  inda  wani zaubin  su  ke  bayyana  korafin cewa gara jiya da yau. Ma’ana har yanzu akwai sauran rina a kaba. A nata bangaren, cibiyar yan jarida ta kasa da kasa (IPC) mai mazauni a Lagos, ta tarayyar Nijeriya, ta wallafa jedawalin wasu alkawuran da ta ce shugaban kasa Buhari ne ya yi ga yan Nijeriya a lokacin yakin neman zaben 2019.

Cibiyar  ta kara da cewa Buhari ya yi wa yan Nijeriya sabbin alkawura 30, wadanda su ka shafi ci gaban kasa, da su ka hada da alkawarin  shimfida  hanyoyi  da layukan dogo, bunkasa sha’anin ilimi, noma, yaki da talauci, bai wa mata da matasa kaso mai tsoka a gwamnatin shi, yaki da cin hanci da karbar rashawa, kana da uwa uba matsalar tsaron da ta addabi Nijeriya.

ugu da kari kuma, ya dauki alkawarin samar wa da matasan da su ka gama makaranta miliyan daya aiki a karkashin N-power da karin wasu sama da miliyan 10 ayyukan da aikin fadada ciyar da yara yan f iramari  daga  miliyan  9.3  zuwa 15, wanda zai taimaka wajen habaka masu sana’ar tuwo-tuwo 300,000 da aikin noma.

Bai  wa  kananan  yan  kasuwa bashi mai sauki na naira miliyan daya ga kananan yan kasuwa, kana da kara adadin yan kasuwa da za su ci gajiyar bashi a karkashin ‘Trader Moni’ da ‘Market Moni’, hadi da ‘Farmer Moni’ daga miliyan 2.3 zuwa miliyan 10.

Ya sha alwashin cewa gwamnatin shi za ta bai wa matasa mukaman ministoci da mataimaka na musamman da sauran ma’aikatu da hukumomi. Tare da bai wa mata kaso 35 cikin dari na yawan mukaman gwamnati.

Buhari ya dauki alkawarin horas  da  malaman  firamari  da sakandire  don  tafiya  kafada da kafada da fasahar zamani, sannan da samar da kayan aiki a makamantu 10,000 a kowace shekara.

Haka kuma ya dauki alkawarin kammala ayyukan hanyoyin  mota  365  wadanda aikin su ke gudana a fadin kasar nan. Sannan da bunkasa masana’antu 6 da za a gina a shiyyoyi shida da ake dasu a kasar nan. Daga cikin alkawuran sun had da daukar matakin hana jami’an gwamnati zuwa kasashen waje neman magani. Da sake farfado kamfanin karafa na Ajaokuta. Gwamnatin APC ta sha alwashin samar da wutar lantarki ma’aunin megawatt 20,000 cikin shekaru hudu, tare da kara adadin zuwa 50,000 don bunkasata nan da shekaru 10 masu zuwa. Da samar da ayyukan yi miliyan uku kowace shekara ga yan Nijeriya, sannan da  tallafa  wa  maras  karfi  miliyan 25 da naira 5000.

A nata bahasin, kungiyar sake farfado da ci gaban Nijeriya (NNC), ta bayyana mahangar ta dangane  da  gwamantin a yankin arewacin Nijeriya, lamarin da ya jawo sakwantar daruruwan rayukan jama’a. shugaban kasa Muhammadu Buhari, cikin shekaru biyar, ta ce salon yadda gwamnatin ke gudana bai saba ka’ida ba, duk da tarin matsaloli da kalubalen da take fuskanta.

Ta sanar da hakan a wata takardar sanarwar bayan taron ta, mai dauke da sa hannun shugaban  ta  Mista  Adeola Adewunmi da Sakataren sa Olutunbosun Osifowora, mai taken: Shekaru biyar na gwamnatin Buhari, nasarori, matsaloli  da  kalubale;  kungiyar ta ce gwamnatin Buhari ta yi kokari wajen yaki da annobar korona, rage farashin kudin man fetur, salon farfado da f itar  da  kasar  daga  cikin  matsin tattalin arziki duk su na daga bangarorin da ya yi kokari. Amma NNC ta nuna gazawar gwamnatin ta fuskar yadda ta ke  ciyo  bashi  don  aiwatar  da wasu ayyukan da ba su da riba a tsarin tattalin arziki, kuma babu  takamaiman  tsari  tattare dashi.

Haka  kuma  NNC  ta  bayyana bacin ranta dangane da yadda ake samun takunsaka a tsakanin ma’aikatu da hukumomin gwamnatin Buhari, tare da saba misali da tata-burzar da ta kaure tsakanin ministan sadarwa Malam Isa Pantami da  Hon.  Abike  Dabiri-Erewa, shugabar hukumar ‘Nigerians in Diaspora’ inda kungiyar ta ce wannan bai dace ba.

Har wala  yau NNC ta bayyana rashin jin dadinta dangane da tabarbarewar  sha’anin  tsaro  a baya bayan nan, musamman Babbar jm’iyyar PDP mai adawa a Nijeriya ta bayyana shekaru biyar na mulkin APC a karkashin gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin wadanda ba su da wani amfani.

PDP ta bayyana hakan ne a cikin wata takardar sanarwa mai cauke da sa hannun sakataren ta na yada labarai, Kola Ologbodiyan, ranar Jumu’a, inda ya kara da cewa, Buhari ya  mayar  da  Nijeriya  baya,  na shekaru 60 da su ka gabata. Mista Kola ya kara da cewa, “Bisa wani binciken da mu ka gudanar ta hanyar tuntubar mafi yawan  yan  Nijeriya,  jam’iyyar mu ta gano yadda gwamnatin Buhari ta keto shekaru biyar ba tare da aiwatar da wani abin a zo a gani ba, a gani na bai wuce a kira ta da mai tashen fara ba.” “A  wajen  jam’iyyar  mu,  ranar 29 ga watan Mayu a karkashin gwamnatin Buhari, rana ce da alhini, nuna rashin kwarewa, jagoranci ba alkibla tare da yadda cin hanci da karbar rashawa ya yi katutu a manyan jami’ai kuma a hannun gwamnatin yan farfagandar abinda ba a yi ba.”

“A karkashin gwamnatin shugaban kasa Buhari, 29 ga watan Mayu ta kasance ranar bakin ciki ga yan Nijeriya, ranar rashin cika wa yan kasa alkawuran  da  lissafin  shibcin gizo a nasarorin da babu su a kasa ga yan kasa.” PDP ta kara da cewa, “wannan gwamnati ce wadda ta gaza warwas a manyan matsalolin gudanar da mulkin kasa, wadanda  su  ka  hada  da  tsaro, farfado da tsarin tattalin arziki tare da yaki da rashawa.” “A cikin wadannan shekaru biyar, gwamnatin APC babu abinda a zo a gani da ta tabuka ga kasar mu, kama daga dukan alkawuran da ta dauka, na habaka ci gaban kasa, wadata  manoma  da  kayan aiki, gina manya da kananan masana’antu, darajar naira, habaka hanyoyin ayyukan yi ga matasa, al’amarin da ya mayar da kasar mu mai kan cin bashi daga kasashen waje.”

“A cikin wadannan shekaru biyar na mulkin APC, shugaban kasa Buhari ya yawace kasashen duniya wajen cin bashi.” Yan Nijeriya da dama sun tofa albarkacin bakin su dangane da cikar gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari shekaru biyar a karagar mulkin, inda wa su ke bayyana matukar rashin jin dadin su bisa tabarbarewar sha’anin  tsaro,  musamman  a yankin arewacin Nijeriya.

Haka  zalika  kuma,  wasu  da dama sun caccaki gwamnatin APC da rashin iya mulki, sun nuna yadda abubuwa su ka sukurkuce da shiga matsin tattalin arziki, wanda yan Nijeriya su ka ce ba su taba ganin irin sa ba. Haka  kuma, ba a taru aka zama daya ba, yayin da wasu ke kallon asara, wasu kuma riba su ka hanga a salon mulkin jam’iyyar APC a Nijeriya.

Exit mobile version