Ibrahim Muhammad" />

Gwamnatin Buhari Ta Yi Nasarar Kawo Gyara Ga Matsalolin Kasar nan -El-yakub

HON. UMAR EL-YAKUB jigo ne a jam’iyyar APC. Kuma tsohon dan majalisar wakilai ta tarayya daya taba wakiltar Birnin Kano. A wannan hira ya bayyanawa IBRAHIM MUHAMMAD irin rawar gani da Gwamnatin Buhari ta yi wa kasar nan, musamman don kyautata ci gabanta. Ga yadda hirar ta kasance:

A matsayinka na daya daga jigo a jam’iyya me mulki ta APC zuwa yanzu tun daga kama mulkin Buhari kusan shekaru uku a matsayinka na dan jam’iyya kana ganin kwalliya ta samu biyan kudin sabulu bisa zabenda a ka yi mata?

A’uzu billahi minas shaidanir rajim. Bismillahir rahmanir rahim. To alhamdu lillahi dukkan godiya ta tabbata ga Allah madaukakin Sarki.

Babu shakka wannan tambaya taka akan gaba take kuma amsar shi ne, eh mun gode Allah kwalliya ta biya kudin sabulu , saboda ko babu komai an sami canje-canje na kwarai, ingantattu wanda suka kawo tsari na gyara na tabbatarda dorewar ci gaban al’umman Nijeriya ta bangare daban-daban. Misali kamar yadda koda yaushe nasan kukanji, kukan gani kuma abu ne wanda ya ke da muhimmanci a jaddada shi harkar tsaro, babu shakka har yanzu akwai barazana iri-iri da sauransu a wurare daban-daban, amma akan gaskiya kai ka sani ni na sani, yawanci wadanda suke zaune a Arewacin kasar nan har a wannan gari namu na Kano da jihohin arewa maso gabas irin barazanar da muka gani.

Irin zaman da muka yi na fargaba da tsaro da rashin walwala da kowa hankalinsa ba a kwance yake ba cikin tsawon lokaci. Bana mantawa kamar yadda ake cewa filin dagar yaki haka muka zama a garuruwammu masu babura sai sun sauka sun tura, shingen bincike a wannan garin namu na Kano in an ce ya kai 70 ba mamaki ba zan manta ba ko’ina ka je ‘yan sanda, idan kana tafiya ko leda ka gani a hanya tsoro kake kana tunanin ko bam aka saka. Masallatai da makarantu tsoron zuwa ake majami’u ma kiristoci tsoron zuwa suke. Ba wanda ya ke da kwanciyar hankali da natsuwa balle ma ya je yayi al’amuransa na yau da kullum. To wannan ba karamar nasara ba ce da wannan Gwamnati tamu ta yi.

Idan ka tafi zancen harkar noma kowa ya sani daga shigowar Gwamnatin Buhari zuwa yanzu an sami gagarumar nasara yanzu dani dakai watakila bazamu iya kirga wadanda suka shiga noman shinkafa da sauran al’amura daban-daban na noma ba, kowa ya koma yana cewa ashe noman nan da muka bari ba karamin alheri bane a cikinsa zai cida al’umma kuma zai kawowa mutane aikin yi da sana’oi kuma muna ganin canji muna ganin gyara.

Na dan dade ban yi tafiya ba daga Abuja zuwa Kano a mota yawanci na kan shiga jirgi, amma da na yi kwanan nan sai na kara gode wa Allah da murna da sha’awar yadda na ga wurare suna ta tasowa na noma ne ko kuma inda ake sarrafa amfanin gona duk ga su nan sai kara bunkasa suke, kuma mutane da yawa sai sha’awar shiga suke har mutanen kasashen waje da wanda suke nema su kawo kudinsu kasar nan su sa a harkar noma ga manyan masu kudinmu, irinsu Dangote da sauransu kusan yanzu jihohin arewacin kasar nan kowa kokari yake ya zuba kudi masu yawa a bunkasa harkar noma da kiwo, to wannan babbar nasara ce, saboda shi ne zai ci gabantar da jama’a ya kubutar damu daga kangin talauci kuma ya bada sana’a da aikinyi ga miliyoyin yan Nijeriya wanda Gwamnati bazata iya basu wannan sana’ar ba, kuma ba wani abu dazai kawo sana’a mai yawa face irin wadannan ayyuka na gona da bunkasa masana’antu da sukeda alaka da harkar noma.

Sannan harkar gine-gine in aka duba ana samun canje-canje da ci gaba, yanzu ana buga sabon layin jirgin kasa daga Legas zuwa Ibadan wanda zai zo harkano, kuma kwanannan za a fara daga Kano ya tafi Kaduna dan a hada da wuri, haka shugaban kasa ya fada a bayaninsa kwanannan, saboda haka ba karamar ci gaba bane idan aka sami layukan jiragen kasa suna gangarawa ko’ina a cikin kasar nan ana diban mutane da kayayyakinsu ba karamin bunkasa tattalin arziki bane, haka harkar ilimi kanta an sami daukikala-kala wanda Gwamnatin tarayya ta shigo ciki da kuma Gwamnatocin jihohi, karka manta idan a ka yi zancen Gwamnatin APC ba za ta tsaya kawai ga akan Gwamnatin tarayya kawai bane harda suma Gwamnatocin jihohinmu na APC dana kananan hukumomi tunda abin hadaka ce ayyuka daga sama zuwa kasa ko daga kasa zuwa sama ya danganta yadda ka duba al’amarin, to shi kansa wannan a Gwamnoninmu ma sai sam barka dan da damansu sun yi abubuwa na a zo a gani musammam ma harkar noman nan tunda bamuda abin da ya fi noman nan, tunda ba za a ce kowa yana da mai ba ko ma’adinai , to a ma’adinan ma wannan gwamnati ta kara himma wajen azo ayi tsarin hakosu dan ci gaban al’umma saboda haka fanni daban-daban ina tabbatar maka an ci nasara Mutuncimmu na yan Nijeriya a idon Duniya ya canza, ba kamar daba da ba a daukarsu da kima da mutunci, wanda yanzu Buhari ya kara mana kwarjini da martaba saboda irin girmamawa da ake dashi a kansa a kasashen Duniya na ganin mutumne mai kamala, mutunci ba barawo ba, me kishin al’ummarsa.

Idan ka duba wajen barnatar da dukiyar al’umma wanda da ake yi a kazamce kamar babu gobe shi kansa wannan an sami sauki na cin hanci da rashawa, ba zance an daina ba, dan babu inda za ace an rasa irin wannan amma dai an sami sauki, muna fata a yi ta samun sauki dan mutane su gane babu alkhairi a cin hanci da rashawa kuma yana cutarda al’umomi da fatan wadannan abubuwa mutane za su fuskancesu su gane an sami nasara.

Ba za a ce duk abin da a ke so a wanzar ya wanzu ba a sherannan uku dan shekaru hudu ma bashida yawa a wajen gyara. Barna ce nan da nan sai ka yi ta amma gyara abune da yake daukar lokaci saboda haka babu shakka shi yasa muke fata a kara ba shugaban kasarmu dama dashi da ragowar Gwamnatocimmu na jihohi a sake ba APC dama idan Allah ya yarda abin da muka fara na ci gaban al’umma na gyara tattalin arzikin kasa muna gani zai dore a samu nasara.

To kuna maganar an sami tsaro amma mutane suna kukan Gwamnatin ta sakasu a tsadar rayuwa fiye da baya da ake samun sauki fiye da yanzu, bayan zaton cewa zuwan Buhari sunasa ran samun saukine fiye da baya sai gashi tsadar na ninkawa me za ka ce gameda wannan?

To idan aka ce abin yana ninkawa ba a yi adalci ba, wani abin ya karu amma wasu abubuwan sun ragu babu shakka. Yanzu saboda Allah kudin shinkafa da ake sayarwa da da yanzu daya ne? Ai an sami sauki , haka ne? Tambayarka nake malam Ibrahim ko baka saya ne? Tambaya nake maka ka amsa mana, (dariya)Ya kaki amsawa, to an sami sauki a wasu kayayyakin kuma gyara ita takeda wahala, ai dama wannan abin sai an dan sha wahala za, a sami sauki.

Saboda irin barnar da a ka yi ta baya da ginshikin tattalin arzikinda aka ragargaza na kasa saboda barna da sata da rashin tsari mai inganci mai dorewa shiya jawo irin wadannan abubuwa ke faruwa amma insha Allahu muna ganin za a rika samun sauki tunda an dauki hanyar gyara. Wani abin in yazo na gyara dama sai an sami dan kunci amma baai zama mai dorewa ba a yardar Allah.

Tunda idan aka gyara tattalin arziki, mutane suka sami aikinyi aka habaka kasuwanci da noma to za ka ga cewa abubuwa da kansu sai suzo su rika saukowa , wanda abin zai shafi al’umma gaba daya. Ban yarda ace matsuwar tafi daba an sami sauki an sami raguwa yanzu misali kamar kayyayakinda ake shigowa dasu da kasar nan, na yarda lokacin Janaton tunda an sami kudi masu yawa aka yita barnatawa daidai da Dala yadda ake sayenta bata kai yanzu ba amma kar a manta fa saida Dala takai sama da N500 amma yanzu ta sauko N300 da wani abu,  to ashe an sami dan sassauci ba kamar baya ba, to a hankali muna fata zata sauko saboda yawan abin da muke fitarwa da yawan kudi da yake shigo mana ba kawai ta mai ba ta harkar noma da ma’adinai da yawan bunkasar masana’antu shi zai sa dalar ta rinka saukowa saboda muna kawota da dama ta fitarda abubuwa da yawa sai kuma a sami sauki. Saboda tsadar dala wani sa’in in aka sayo kayan masana’antu za ka ga saboda tsada da yadda ake gudanar da masana’antu za kaga kayan sukan yi tsada , amma sai kaga cewa yanzu saboda ana yi din da yawa a hankali sai ya rika saukowa.

Abin da ya faru da mun wofintar da kasarmu ne mun yarda kawai mu shiga da komai saboda haka akazo aka rika kawo mana aka kashe masana’antu shikenan , misali akwai masana’anta da kayadda take ace na miliyan 100 ne, amma dana daukar ma’aikata 30 ko 40 da suke samun kudin shigowa, amma saboda kayadda take na miliyan 100 anje an kawo kayan miliyan 200 irin wannan na miliyan 100 anje an kawo kawo daga waje. Mutun daya sai ya kawo kayan miliyan 200 irin wannan na miliyan 100, zai kawosu ne akan idan kai kana sayarwa a N10 shi sai ya sayar N8 saboda basuda biyan ma’aikata, kuma ya sayo kayan da araha, idan ana haka sai kaga kanfanoninmu da suke ba mutane aiki an kashe su, sai mutun daya ya kashe sana’ar mutum 100 wanda da anayin sana”oin dasu wadannan mutun 100 sun sami kudin shiga a hannunsu da za su kulada iyalamsu kuma su shiga kasuwa suyi amfani dasu amma sai kudin ya koma hannun yan’tsirarun mutane duk kuwa da mutane suna gani sun sami sauki , amma saukin ya dauke musu kuma nasu”Purcharsing power”Basu ganeba abin da ya faru kenan a baya barna ce shi ne ake gyaranta sai a hankali tattalin arziki yana kara gyaruwa yana habaka sannan mutane su yita samun sauki kuma tunda saukin an ginashi kan turba ta gaskiya sai ya ama mai dorewa.

Akwai masu cewa ayyana muradin takarar Buhari a karo na biyu ba wani abu azai canza koda ya sake dawowa saboda rashin gamsuwa da mulkinsa a wannan karon kamar yadda masu hamayya ke fada kanada ja akan hakan?

Dama yaya za ayi dan hamayya ya gamsu. Su ba so suke a barsu su yita badakalarsu yadda suka saba dama sun kashe kasa sun sace duk kudin mutanen kasa anzo ana badakala da”Impunity”Babu doka babu tsari babu sanin yakamata, to kuma yaya za suso wanda zai kawo gyara ya tottoshe wannan barna tasu ai dama baza su soba, kuma basu suka haifa mana wannan bala’in ba shekaru da yawa da suke mulki. Kuma karka manta Allah ya taimakemu yaba shugaban kasarmu lafiya tsawon lokuta wanda shi kansa wannan ya dan dakila wani abu da za a samu na irin aikinda zaiwa mutane a wannan lokacin, saboda haka yanzu Allah ya bashi lafiya kowa ya yarda an fara samun canji da gyararraki akan al’umura. Mu muna fata mun kuma sani Allah zai taimake mu ya bashi karo na biyu cikin koshin lafiya ya bashi mataimaka nagari da za a ci gaba da yin aiki fiye da baya.

To wace shawara ka ke da ita ga al’ummar Nijeriya?

A yi hakuri a ci gaba da yi wa shugaban kasa muhammadu Buhari addu’a ya kara lafiya kuma Allah yayi masa jagora su ci gaba, dan alkhairin ci gabansu shi ne alkhairin ci gabammu, gyaransu shi ne gyarammu saboda haka ba zance bane na a yi ta batanci, tsinuwa da addu’a mummuna, a’a zance ne na ayi musu addu’a tagari a sami jagorancinsu ingantacce. Ina kira ga yan Nijeriya idan Allah ya kawomu 2019 a kara marawa shugaban kasa Muhammadu Buhari baya da jam’iyyar APC da yardar Allah za mu kara tabbatar da gyara da ci gaba mai dorewa mai inganci yadda yan’baya yadda za su amfani abin da suka shuka.

Exit mobile version