Abubakar Abba" />

Gwamnatin Buhari Ta Zuba Jarin Dala Biliyan 10 Akan Ayyuka –Osinbajo

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya sanar da cewa gwamnatin tarayya ta zuba jarin kusa da dala biliyan goma akan ayyukn samar da ci gaba a cikin shekaru uku da suka shige.
Yemi ya ce, zuba jarin ya mayar da hankali ne akan aikin hanyoyi da samar da wutar lantarki da aikin layin dogo, wanda duk an samu gagarumar nasara.
Mataimakin shugaban kasar ya sanar da hakan ne a jawabin sa lokacin bude taron masu zuba jari kai tsaye na kasa da hukumar habaka zuba jari ta kasa (NIPC) ta shirya a birnin Abuja ranar talatar data gabata.
A cewar sa,“ a shekaru uku da suka wuce mun zuba jarin kusa da dala biliyan goma wanda wannan babban kudi ne da aka zuba akan aiki tun a shekararsince 2016.
Yemi yaci gaba da cewa, “abinda muka mayar da hankali shi ne aikin hanyoyi da samar da wutar lantarki da sabon aikin layin dogo kuma duk wannan zai taimaka wajen kara samar da kasuwa da rage kashe kudi akan kasuwanci.”
A cewar sa, labarai mai dadi shi ne Nijeriya ta fita daga cikin kangin tattalin arzikin kasa kuma Nijeriya a shirye take fiye da haka don ganin bata sake rasa samun dama ba.
Yemi ya ce, gwamnati ta mayar da hankali akan aikin noma wanda ya samar da zuba jarin daloli a cikin shekaru uku da suka wuce akan ma’aikatar sarrafa shinkafa da noman sikari da masana’antar sarrafa taki da sauran su.
Ya bayyana cewar, asusun ajiyar Nijeriya na kasar waje ya kai kimanin dala biliyan hamsin, wanda a lokacin da wannan gwamnatin tazo ta iske dala biliyan talatin ne.
A cewar sa, “kudin mu na rarar mai a shekaru biyu da suka wuce shi ne karo na farko da aka samu kudin shiga tun lokacin da aka kafa a shekarar 2011.
Yemi ya ce,“mun kara habaka sabon haraji daga miliyan biyar zuwa miliyan sha hudu a shekarar 2016, inda a yau ya kai miliyan sha tara wanda duk wannan kokari ne na inganta samar da kudin shiga.
Ya ce, damar da gwamnatin tarayya ta samu, ya biyo bayan samar da tsari har da yawan alumma wanda shi ne mafi girma a Afirka da kuma rabin nahiyar Afirka.
Yemi ya ce, Nijeriya tana da yawan matasa a duniya inda suka kai kasha hamsin bisa dari wadanda suke masu kasa da shekaru ashirin da suka kai kashi saba’in da biyar da kuma masu shekaru talatin da biyar.
Ya yi nuni da cewa, yana da sauki ko wacce kasa data damu da alkiblar ta kamar yadda muma a Nijeriya muke da dama da yawa.
A watan Disambar da ya gabata an bude kamfanin sarrafa hatsi mai suna Kellogg a jihar Legas samakon hadaka da da wani kamfanin Amurka da kuma wani kamfanin rukunoni mai suna Tolaram dake kasar Singapo.
Sai dai, Yemi ya ce, kamfanin Kellogg ya kai sama da shekaru dari kuma a wannan ne karo na farko da ya zuba jari a Nijeriya.
A cewar sa, bayan kimanin rabin shekara tuni suna shirin kara fadada tsarin su ganin cewar sabon kamfani ya kai yawan da ake bukata.
Yemi ya sanar da cewar, akwai da dama da aka ci nasara wajen yin hadaka tsakanin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu.
Ya yi nuni da cewa, babban misali shi ne kamfanin LNG, na sarrafa gas don fitar dashi a daukacin kasuwannin kasashen duniya don a taimakwa Nijeriya wajen samun kudin shiga.
A cewar sa, kamafin mai zaman kansa wanda kuma mallakar manyan kamfanoni uku ne, inda kuma kamfanin NNPC yake take masu baya.
Ya sanar da cewar, babban mahimmanci shi ne, gwamnati ta samu damar samar da kyakyawan yanayi na kasuwanci.
Yemi ya ce, gwamanti ta kaddamar da shirye-shiye da dama don inganta zuba jari saboda tsare-tsaren ta, musamman ganin cewar Bankin Duniya ya amince da Nijeriya a matsayin wadda ta kai ta goma wajen bunkasar tattalin arziki a duniya.
Ya bayyana cewar, hukumar bayar da lamuni ta duniya (IMF) ta buga misali akan cewar samar da kyakyawan yanayin kasuwanci da tsari sun taimaka matuka wajen fitar da tattalin arzikin kasa ya yi daga karayar tattalin arzikin kasa a shekarar data gabata.
Ya yi nuni da cewar, abinda yafi birge mu shi ne saboda tsare-tsaren aka kirkiro na gano sahihan masu zuba jari wanda a baya suka zama turniki saboda yadda ake samun kalubale wajen aiwatar da ayyukan gwamnati.
A tsarin na farko an mayar da hankali akan zuba jarin dala 22.5, inda kuma kimanin dala biliyan goma na yawan ayyuka tare da samar da aikinyi da ya kai 500,000 nan da shekara 2020 mai zuwa an ware su wanda kuma za a iya tafiyar dasu a cikin sauri.
Yemi ya yabawa hukumar NIPC, inda ya ce, a cikin watanni sha takwas da suka shige, bata bar kowa a cikin kwankwanto ba wajen sauke nauyin da aka dora mata ba na karawa masu son zuba jari a Nijeriya kwarin gwaiwa.
Yemi ya ce, hukumar ta hada cikakken bayanai akan masu zuba jari a Nijeriya, inda hakan zai baiwa wadanda tuni suka zuba jari a kasar damar samun dukkan bayanan da suke bukata a cikin sauki.
A cewar sa, hukumar ta kuma kaddamar da yanar gizon ta don samun dukkan bayanan da ake bukata akan fara gudanar da kasuwanci da dokoki da haraji.

Exit mobile version