Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya umarci babban akanta na kasa da ya dinga bayyana wa ‘yan Nijeriya adadin kudaden da suke shiga lalitar gwamnatin tarayya da wanda ke fita daga lalitar a kullum.
Shugaba Buhari ya ba da wannan umarni ne a ranar Litinin, 9 ga watan Disamba yayin taron kaddamar da dokoki da tsare-tsaren fayyace hada-hadar kudi na gwamnatin tarayya, inda ya umarci babban akantan ya wallafa rahoton duk wani kudi da aka bai wa kowacce hukuma da ma’aikata da ya haura naira miliyan 10.
Jaridar Premium Times ta ruwaito shugaba Buhari wanda ya samu wakilcin karamin ministan Neja Delta, Tayo Alasoadura ya ce rahoton ofishin babban akantan Nijeriya ne zai dinga sanar da ‘yan Nijeriya adadin kudaden da gwamnati ta bai wa hukumominta da ma’aikatunta domin su gudanar da ayyuka, da kuma sanin adadin kudin da ya shigo musu.
Wakilin Buhari ya ce manufar tsarin shi ne baje ta a faifai kowa ya gani tare da yin keke da keke a harkar tafiyar da kudaden al’umman Nijeriya ba tare da wani boye-boye, kumbiya-kumbiya, lumbu-lumbu ko muna-muna ba.
Bugu da kari, shugaban kasa ya ce bayanin da za’a dinga wallafawa zai kunshi musabbabin bayar da kudin ko kashe kudin, adadin kudin da kuma wanda ya biya kudin ko aka biya kudin, sa’annan sabon tsarin ya tilasta ma hukumomi da ma’aikatu su tabbatar da wallafa duk wata harkallar kudi da ta haura naira miliyan 5.
Haka zalika Buhari ya umarci dukkanin hukumomi da ma’aikatun gwamnati su wallafa yanayin aiwatar da kasafin kudinsu a kowanne kwanaki 7 na karshen kowanne wata, inda bayaninsu zai hada da ayyukansu da kuma amfanin da suka kara ma tattalin arzikin kasar.
Baya ga wallafa kudaden da suka shigo ma gwamnati da wanda suka kashe, shugaba Buhari ya umarci babban akanta na kasa ya dinga wallafa matsayin asusun gwamnati bayan kowanne watanni 4, sa’annan a karshen shekara ma haka.