Injiniya Saleh Mamman Ministan Hasken Wutar Lantarki A Najeriya ya bayana cewa kafin Gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta kamala wa adinta na biyu a 2023 Gwamnatin zata samar da karfin hasken wutar lantarki mai karfin migawat sama da Dubu 11 , A Najeriya. Ministan ya bayana haka ne alokacin da yake zantawa da wasu kafafan hada labarai kai tsaye a daran Laraba a burnin kano.
Har ila yau ya ce yanzu haka Najeriya na da karfin migawat 5520 wanda a tarihin Najeriya ba a taba samun wanan adadi ba sai a zamani shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda yanzu hasken wutar lantarkin ya karu fiye da da wanda ya ce kafin zuwan wanan Gwamnati wutar bata wuce 3000 da duriya dan haka ansamu karin samun wuta sai dai kawai inda suke da matsalar Taransufuma ko wani abu mai kama da wanan a yanzu.
Haka kuma ya ce yanzu haka akwai yarjejeniya tsakanin Najeriya da kasar Jamus wada ta kaita Uro Billion biyu dan samar da wada taken wutar lantarki a Najeriya dan ga ne da aikin samar da wutar lantarki na Manbila ya ce a nanan ansa dan ba kuma aiki ne da za ayi ba wata matsala musamam ganin aikin na yan kasuwa ne da hadin kan Gwamnati ba wata matsala da zai samu a wanan karan a cewar Minista Injiniya Saleh Mamman,
A karshe dai ya ce Gwamnatin Buhari na kashe kudi Naira Billiyan 50 duk wata na kudi wutar lantarki da take biya a yayin da kamfanin dilacin wutar lantarki na Disco, ba sa iya biyan sama da Billiyan 10 a duk wata wanda yanzu haka Gwamnati na bin Disco sama da Naira Tiriliyan guda wanda kuma ita Gwamnati ba za ta yadda Disco, ta kara Kudin wuta ba sai sun cika dukkanin sharudan da Gwamnatin Muhammadu Buhari ta samu su na samarwa da jama`a wutar lantarki a Najeriya.