Daga Abubakar Abba
Wakiliyar kasar Faransa a Afrika ta Yamma Dakta Sonia Darrack ta danganta shirin farfado da aikin noma da gwamnatin jihar Kwara ta kaddmar a kwana baya na ATP daga shekarar 2020 zuwa shekarar 2030 a matsayin babbar dabara ta habaka fannin noma don riba a jihar.
Ta ce, ta na da yakinin cewa hakan, zai kuma kai har ga zuwa sauran fanonin dake a jihar, harda fannin samar da ilimin zamani da kuma bayar da horo a fannin aikin noma a jihar, inda ta kara da cewa, ga dukkan masu son zuba jari a fannin aikin noman jihar ya san gwamnatin jihar ta samar da kyakyawan yanayi na yin noma.
Ta kara da cewa, hakan zai kuma kara wa masu son zuba jari a fannin aikin noma na jihar Darrack, wacce kuma ita ce, Kansilar kula da aikin noma ta shiyya ga kasashrn Benin, Kkmaru, Ghana, Nijar, Nijeriya da kuma Togo a ofishin jakadanci na kasar Faransa ta sanar da hakan ne a yayin da ta kai ziyarar aiki a jihar ta Kwara.
“Shirye-shirye na nan tafe daga gun kamfanoni masu zaman kansu a kasar Faransa domin yin hadaka da gwamnatin jihar Kwara a kan fannonin da ban da ban na noma da kuma kiwo, inda ya kara da cewa, za a samar da kayan aikin noma na zamani da kuma habaka noma don riba a jihar.”
Ta ci gaba cewa, “Ganin cewa gwamnatin jihar ta samar da kyakyawan yanayi na kasuwanci a jihar ta Kwara, tuni akwai kamfanonin kasar ta Faransa masu zaman kansu dake da sha’awar zuba jarinsu a cikin fannin aikin noma a jihar, musamman a bangarorin kiwo, samar da abincin dabbobobi kayan aikin noma na zamani da sauransu.
Ta bayyna cewa, “Samar da hanyoyin isar da sako na zamani zai rage yawan asarar da manoma ke yi yayin gibin amfanin gona, kara taimaka wa wajen habaka fannin aikin noma da kara wadata kasar nan da abinci .
Darrack ta kara da cewa, hadakar da gwamnatin jihar Kwara ta yi da gwamnatin kasar Faransa kan bayar da ilimin aikin noma ta hanyar yin amfani da wasu kwalejojin dake koyar da Ilimin aikin noma a Kwara, hakan zai kara karfafa fannin aikin noman a jihar.
Ta kara da cewa, wannan hadakar ta hada harda masu ruwa da tsaki na waje da na kuma a tsakanin makarantun wajen bayar da horon da ya da ce a fannin.
Darrack ta sanar da cewa, hadaka da gwamnatin jihar Kwara an faro ta ne a watan Fabirairun shekarar 2020 a lokacin da Gwamnan jihar AbdulRahman AbdulRazak ya halarci taron baje kolin kayan amfanin gona nan kasa da kasa da ake gudanar a kasar Farisa.
Ta kara da cewa, lokacin da gwamnan ya halarci taron baje kolin na Farisa da aka gudanar a watan Fabirairun shekarar 2020, mun yi samu yin amfani da damar wajen tattauna wa dashi kan yin hadaka a fannonin aikin noma da ban da ban na jihar Kwara, inda muka nuna sha’awar yin aiki tare.
A cewar ta, sai dai abubakar wa sun tsaya chak a lokacin bayan bullar annobar Korona a sassa da ban da ban a kasar, amma bayan da a kwanan baya gwamnan ya kai wa Jakadan kasar ta Faransa, ya bukaci yin hadaka da kasar ta Faransa a fanonin aikin noma da dama na jihar da kuma kara bunkasa aikin noma don riba a jihar.