Rabiu Ali Indabawa" />

Gwamnatin Gambiya Ta Mayar Da Martani Zuwa Jammeh

Gwamnatin kasar Gambia ta yi Allah wadai da barazanar tsohon shugaban kasar Yahya Jammeh na cewar yana shirin komawa gida daga Ekuatorial Guinea, inda ya samu mafakar siyasa yanzu haka.
Hirar da aka yi da tsohon shugaban da aka nada ta waya, ake ta kuma yadawa ta kafar sada zumunta, ta ruwaito Jammeh na cewa babu wani mahaluki da zai hana shi komawa Gambia.
Gwamnati mai ci ta bayyana kalaman tsohon shugaban a matsayin yadda ya matsu ya zama mai fada aji kan harkokin siyasar Gambia, duk da cigaba da tattara bayanan cin zarfin Bil adama da kuma almubazzaranci da dukiyar jama’a da ake yi domin kai shi kotun duniya.
Bayan kwashe shekaru 22 a karagar mulki, shugaba Adama Barrow ya kada Jammeh a zaben da aka yi a shekarar 2016.

Exit mobile version