Alhaji Ali Baba Fagge shi ne babban maitaimaka wa gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje kan harkokin Addini, gogarman kare kimar gwamna da gwamnatin APC, allurar dinke barakar dake tsakanin mabiya addinai da dariku daban daban a Jihar Kano. Atattaunawarsa da wakilinmu a Kano Abdullahi Muhammad Sheka, Ali Baba ya bayyana farin cikinsa bisa yadda Kanawa suke nuna gamsuwa ga kabakin arzikin da gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje ke yi musu sannan kuma ya yi tsokaci kan masu yi wa gwamnatin ta su kallon-hadarin-kaji da cewar ahir dinsu. Ga yadda tattaunawar ta kasance;
Bari mu fara da jin wanda muke tare da shi?
Alhamdulillah, godiya ta tabbata ga sarkin da ke bada mulki ga wanda yaso alokacin da yaso, tsira da amincin Allah su kara tabbta ga fiyayyen halitta Annabi Muhammadu (SAW). Ni sunana Ali Baba Fagge wanda aka fi sani da Ali Baba a gama lafiya, maitaimaka wa gwamna Khadimul Islam Dakta Abdullahi Umar Ganduje kan harkokin addinai daban-daban.
Ranka ya dade kafin mu yi nisa ka ce mai taimaka wa gwamna kan harkokin addinai daban-daban, me hakan ke nufi?
Gwamnatin Khadiul Islam daman an san jagoran gwamnatin da himmar taimaka wa harkokin addini, kuma tarihi ya tabbata Ma’aiki (SAW) ma ya zauna da mabiya wasu addinai kuma ana kokarin kare wasu hakkoki nasu matukar ba za su cutar da addini ba.
Ali Baba Jihar Kano jiha ce da al’amarin harkokin addini ke daukar Hankali, shin ko wacce rawa wannan ofishin na ka ke takawa wajen ganin gwamnatin na hidimtawa Musulunci?
Ban san ta inda ya kamata na fara amsa wannan tambaya ba, kasancewar dan da ke cikin gyatumarsa a Kano ma yasan Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje na yin bakin kokari wajen ganin ya sauke nauyin da Allah ya dora masa. Da farko kamar yadda aka san wannan gwamnati karkashin jagorancin Ganduje akwai abubuwa masu tarin yawa wanda ake yi wa jama’a, musamman abin da ya shafi harkokin ci gaban Kano da Kanawa. Haka kuma wannan ofis dana ke jagoranta ofis ne mai tarin albarka kasancewar wadanda muke yin aiki dasu iyayen al’umma ne kuma magada annabawa, malami yana da kima kwarai da gaske, wannan tasa jihar Kano ta samar da wannan ofis domin yin duk abin da ya dace ga malamai da kuma sauran addinai abokan zamanmu.
Wannan ta sa a lokacin da wasu kabilu a wani bangare na kasar nan ke muzguna wa Hausa da Musulmi, mu a jihar Kano abokan zaman mu kowa zaune yake cikin kwanciyar hankali, duk da labaran da ake ji daga wasu sassan kasarnan, Maigirma Gwamna Ganduje ya yi ta gudanar ta tattanawa da shugabanin kabilun da suke zaune a Kano, haka kuma Malamai suntan gabatar da jawaban muhimmancin zaman lafiya. Muna yiwa Allah godiya kowa na ci gaba da gudanar da harkokin sa cikin kwanciyar hankali.
Kana cikin fulogan wannan Gwamnati shin ko wadanne ayyukan za ku iya bugun kirji da su wanda za ku ce kun cika alkawarin da aka yi wa al’umma a lokacin yakin neman Zabe?
Wannan ido ba mudu ba yasan kima ko mai kyashi da hassadar mai hassada dole ya amince da cewar Gwamnatin Ganduje mai fada da cika wa ce, ko a iya ci gaba da ayyukan da aka bar wa gwamnatin a matsayin gado aka tsaya ai kwalliya ta biya kudin sabulu. Misali aikin ci gaba da doguwar gadar saman data fara daga gidan jaridar Triumph ta wuce har Kano club, dubi aikin asibitocin nan biyu na Giginyu da wanda ke kan titin zuwa gidan Zoo. Wadanann ayyuka karasa su bakaramin taimakawa lalitar gwamnatin Kano Ganduje ya yi ba, saboda an fara narka dukiyar Jama’a kuma aka yi watsi da su.
Sanann kuma dubi aikin titin Sheikh Ja’afar Mahmud Adam wanda ake yi yanzu har zuwa Panshekara, dubi gadar Karkashin kasa ta hanyar Madobi da wadda ke kusa da barikin soja na Bukabu, dubi farfado da gidan Jaridar Triumph wanda aka durkusar abaya. Sai kuma yadda gwamnatin ke yin duk mai yiwuwa domin faranta wa ma’aikatan gwamnati da ‘yan fansho sai godiya suke.
Wannan shi ne wai abin dariya yaro ya tsinci hakori, ai duk wanda yasan Gwamna Ganduje ya san mutum ne na kowa da kowa, sanann kuma ba wai malaman addinin musulunci ba, kiristoci ma na jinjinawa Gwamna Ganduje, kana ina kwanakin da suka gabata malamai nawa Gwamnati ta tura saudiya domin yiwa kasa addu’a tare da neman Allah ya karawa shugaban kasa lafiya. Haka kuma kunshin malaman da ke cikin wannan gwamnati aika san gwamnatin ta kowa da kowa ce. Mu abinda muka dauki malamai iyayen kasa wadanda ke iya bai wa kowa shawara, sannan kuma muna godiya bisa yadda malaman ke yi wa gwamnati addu’a ba dare ba rana.
Masu adawa da gwamnatin taku na cewa zango daya Gwamna Ganduje zai yi za su karbi mulki, shin kuna sane da haka?
Su wane ke fadar haka? Kuma suke bada mulki ko Allah, sanann kuma suna ina akayi duk mai yiwuwa wajen dakile takarar Gwamna Ganduje abaya, amma Allah ya ce shi yake bukata kuma shi ya damka wa ragamar mulkin Kano. Wannan shi ake cewa ihu bayan hari mai jiya ta yi balle yau. Kuma Alhamdulillahi Kanawa sun gamsu da ayyukan alharin wannan Gwamnati, masu fadar haka su jira mu hadu a wurin zabe, kuma ai an gwada hakan a wuraren zaben cike gurabun da suka gabata a jihar Kano, wacce nasara suka samu
Muna yi wa jama’ar Kano bushara da cewar kamar yadda aka san jagoranmu ba mutun ne mai son zuga kansa ba, amma ido ba mudu ya san kima, kar a ci gaba da yaudarar ku ana cewa kaza da kaza wanda bai san gari ba to ya saurari daka.
Me za ka ce dangane da cikar Gwamnatin Kano shekara biyu da kuma cikar Kano shekara 50?
Alhamdulillahi wadannan tagwayen bai wa guda biyu cikin daukacin wadanda suka mulki Kano ba wanda ya samu irin wanann bai wa, da farko Alhamdulillahi a lokacin Gwamna Ganduje Kano tayi bikin cika shekara 50, sanann kuma gwamnatin APC ta cika shekara biyu a kan karagar mulki. Haka kuma Ganduje ne kadai Allah ya bai wa hikimar kirkiro da tsarin raba lambobin yabo ga daukacin wadanda suka mulki jihar Kano a tsawon wadannan shekaru 50 masu albarka, aka kuma karrama wasu hamshakan mutane da suka bayar da gudunmawa iri badan daban domin ci gaban Jihar Kano. Wanann ba karamin abin alfahari ba ne, Allah ya hada wa wannan bawa nasa wadanann abubuwa biyu masu dimbin tarihi.
Wannan ta sa a lokacin wadannan tagwayen bukukuwa aka gudanar da abubuwa da aka jima ba a gani a Kano ba, musamman an gudanar da hawan Daba, taruka iri daban-daban da ‘yan kasuwa, masu zuba jari, malamai da iyayen kasa. Haka gwamna Ganduje ya ziyarci gidajen yari inda aka ‘yanta sama da ‘yan bursuna 500 a lokaci guda.
Mene ne sakonka ga al’ummar Kano?
Babban sako na shi ne jama’ar Kano mutane ne wayayyu an daina daure su da igiyar zato, sannan kuma sarki goma zamani goma, jama’a su ne shaida gwamnatin Ganduje ta al’umma ce wadda ke mayar da hankali kan hidimta wa Kanawa, muna kara jadaddawa jama’a tare da bushara kan ci gaba da yiwa Kanawa luguden ayyukan alhairi, muna fatan a ci gaba da yi wa wannan Gwamnati addu’ar fatan samun nasarar sauke wannan nauyi da yanzu abubuwa suke ci gaba da kankama. Muna yi wa Gwamna fatan Allah ya dawo mana da shi lafiya.