Khalid Idris Doya" />

Gwamnatin Gombe Ta Biya Kudin Jarrabawar WAEC, NBAIS Da NABTEB Na Miliyan 204

Yayi Da Ta Amince Da Biyan Ragowar Kudin Tallafin Karatu Ga Dalibai

Inuwa Yahaya

Majalisar Zartaswa ta Jihar Gombe ta amince da sakin kudi har Naira miliyan 204 don biyan kudaden jarrabawar kammala sakandari na WAEC da NBAIS da kuma NABTEB ga fiye da dalibai dubu 13 masu kammala sakandari a bana.

Zaman majalisar wanda Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya jagoranta, ya kuma amince da fitar da kudi Naira miliyan 112 don biyan raguwar kudaden tallafi ga daliban Jihar na shekarun karatu na 2016 da 2017 da kuma 2018.

Da suke yi wa manema labarai karin haske kan sakamakon zaman majalisar karo na 8, kwamishinan yada labarai da raya al’adu Hon. Ibrahim Alhassan Kwami da takwarorinsa na ma’aikatar ayyuka da sufuri Injiniya Abubakar Bappah, da na ilimi Dakta Habu Dahiru, da na albarkatun ruwa Alhaji Mijinyawa Yahaya da kuma na gidaje da bunkasa birane Alhaji Adamu Dishi Kupto, inda suka ce majalisar ta cimma batutuwa ne da za su kyautata zamantakewa da tattalin arziki dama ilimin al’ummar Jihar Gombe.

Kwamishinan yada labaran ya ce: “idan za ku iya tunawa, gwamnatin da ta gabata ta biya kaso 50 cikin dari na kudaden tallafin dalibai na shekarun 2016/2017, da 2017/2018, don haka wannar majalisar ta amince da biyan sauran kaso 50 cikin darin, kuma nan gaba za mu ci gaba da biyan daliban mu hakkokinsu na tallafin karatu.’’

Har yanzu dai game da ilimi, ya ce majalisar ta amince da daga darajar wasu makarantin gwamnati 5 ya zuwa na musamman, daya a kowane yankin mazabar Sanata guda 3 da ake da su a jihar da kuma wasu 2 a fadar jihar kasancerwata alkarya.

Ya ce an yi hakan ne saboda burin Gwamna Inuwa Yahaya na farfado da sashin ilimin jihar cikin hayyacinsa.

A bangaren noma kuwa, kwamishinan yada labaran ya ce majalisar zartaswar jihar ta amince da bada hayan kamfanin sarrafa taki na Jihar Gombe da ake kira Tag Agro kan kudi Naira miliyan 7 duk shekara har na tsawon shekaru 10, ya na mai cewa tuni gwamnatin jihar ta karbi kaso 50 cikin dari na kudin hayan wanda ya kai Naira miliyan 35.

Ya ce an dauki matakin bada hayan kamfanin takin ne don tabbatar da nagarta da karfafa gaskiya a harkar samar da takin zamani a kan lokaci ga manoman jihar baki daya.

Ya kara da cewa majalisar zartaswar ta kuma amince da ware kudi Naira miliyan 250 a matsayin bangaren gudunmowarta a hadin gwiwar da ta yi da gwamnatin tarayya don aiwatar da shirin samar da ruwan sha da kyautata tsabtar muhalli da ake kira PEWASH a takaici don karfafa samar da ruwa da inganta muhalli a Najeriya.

Da yake karin haske kan haka, kwamishinan albarkatun ruwa Alhaji Mijinyawa Yahaya, ya ce an tsara shirin na PEWASH ne don dafawa kokarin da aka yi a baya da na yanzu kan tsare-tsaren samar da ruwa da inganta muhalli.

Ya ce shirin ya kunshi gyaran famfunan burtsate da tona sabi a kananan hukumomin Dukku, da Kwami, da Furnakaye da kuma Balanga, wadanda za su fara cin gajiyan shirin a Jihar Gombe.

Game da tashar motar zamanin da aka yi watsi da ita kuwa, majalisar ta amince da sake bitar kwangilar da aka bayar tun farko daga Naira biliyan 6.028 zuwa Naira biliyan 7 da miliyan 600.

Da yake karin haske, kwamishinan ayyuka Injiniya Abubakar Bappah ya ce tun farko an bada kwangilar ce ga kamfanin da bashi da kwarewar irin wannan aiki, yana mai cewa duba da yawan aikin da ya jibinci aikin injiniyanci da ake kira Cibil Engineering a turance, hakan ya sa majalisar ta sauya kwangilar zuwa ga kamfanin Triacta wanda ke da kwarewa sosai kan tsara irin wadannan ayyuka da aiwatar da su.

Exit mobile version