Daga Khalid Idris Doya
Majalisar Zartarwar Jihar Gombe ta amince da kiyasin kudi Naira biliyan 116 a matsayin hasashen kasafin kudin 2021 da za a tura ga Majalisar Dokokin Jihar Gombe, don nazari da amincewa da shi ya zuwa doka.
Da ya ke karin haske ga manema labarai kan sakamakon zaman majalisar na wannan makon, kwamishinan kudi da bunkasa tattalin arziki na jihar Malam Muhammad Gambo Magaji, ya ce a kasafin na badi an warewa sashin manyan ayyuka Naira biliyan 58.5, yayin da a ka warewa harkokin yau da kullum Naira biliyan 57.8, wanda ya haura kasafin kudin bana da aka yiwa kwaskwarima da kaso 7.5 cikin dari kenan.
A bangaren gudanarwar da ayyukan yau da kullum kuwa, sashen ma’aikata ya samu Naira biliyan 22.7, na dawainiyoyin yau da kullum Naira biliyan 15.7, fansho da giratuti kuwa Naira biliyan 4.1, albashin masu rike da mukamai kuwa Naira miliyan 168, biyace-biyacen bashi kuwa Naira biliyan 14.7, jimilla Naira biliyan 57.5 kenan.
Kwamishinan kudin ya ce kiyasin kasafin kudin 2021 na Naira biliyan 116, ya haura na bana na Naira biliyan 107 da miliyan 609 da 8,500 da kobo 90 da aka yi wa kwaskwarima, da kimanin kaso 7.5 cikin dari.
Ya ce, “Daga cikin Naira biliyan 55.24 na sashin tafiyar da harkokin yau da kullum a kasafin 2020, an kashe Naira biliyan 39.37 tsakanin watan Janairu zuwa Oktoba, wanda ke zama kaso 71.2 kenan cikin dari na kasafin sashin, yayin da daga cikin Naira biliyan 52.37 na kasafin sashin manyan ayyuka a kasafin na 2020, an kashe kimanin kaso 44.8 cikin dari ya zuwa watan Oktoban da ya gabata.”
Ya ce an yi kiyasin samun gibi a kasafin kudin na 2021 da zai kai na Naira biliyan 5 da miliyan 206 da 336, wanda ke zama kaso 4.4 cikin dari kenan na kasafin baki daya.
Ya kara da cewa za a cike gibin ne ta hanyar karbo rance daga ciki da wajen kasar nan, inda za a ranto Naira biliyan 3.5 kimanin kaso 3 cikin dari kenan na kasafin, yayin da rance na cikin gida kuwa zai kai Naira biliyan 4.
Malam Gambo Magaji ya ce tuni gwamnti mika tsarin kashe-kashen kudi na matsakaicin zango da kuma daftarin tafiyar da harkokin kudi ga majalisar dokokin jihar, ya na mai bayyana kwarin gwiwar cewa Gwamna Inuwa zai gabatar da kasafin na badi gaban majalisa a mako mai zuwa.
Da ya ke amsa tambayiyin manema labarai, kwamishinan yada labarai Hon. Ibrahim Alhasan Kwami, ya ce an tsara kasafin kudin na badi ne bisa shawarwarin da masu ruwa da tsaki su ka bayar yayin taron karbar shawarwarin jama’a kan kasafin kudi, irin sa na biyu kenan da a ka yi, ya na mai cewa kasafin yana kunshe ne da bukatu da muradun al’umma.